Ambaliyar Ruwa: Yobe ta buƙaci ɗauki daga Bankin Duniya

0
183

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya nemi Bankin Duniya da ya kawo musu ɗauki tare da ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin gwamnati na samar da hanyoyin magance ambaliyar ruwa da ake sa ran za a fuskanta a wannan damina ta bana.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da harkokin ’yan jaridu na Gwamnan, Mamman Mohammad ya fitar a Damaturu.

Ya  ce, Gwamna Buni ya yi wannan ƙiran ne a lokacin da ya karɓi tawagar Bankin Duniya da na Shirin Acresal da suka kai masa ziyara.

Gwamna Buni, ya ce matakin da ya fi dacewa don daƙile ambaliyar, shi ne gina magudanan ruwa da za su bi da ruwa a garuruwan da ke da wannan matsala a cikin jihar.

“Ya kamata a ɗauki wannan a matsayin wani lamari na gaggawa da kuma muhimmanci ga jama’a don kaucewa barazanar da ke tattare da ambaliyar ruwa da ake tsammanin za a fuskanta a wannan shekara,” in ji Buni.

KU KUMA KARANTA: Muna iya ƙoƙarinmu wajen samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Yobe – Gwamna Buni

Ya bayyana cewa, dole ne a ɗauki ƙwararan matakai don tallafawa da sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu a baya.

Gwamnan ya ƙara da cewa “Dole ne mu goyi bayan juriyar al’umma, da shirin sake tsugunar da su da gwamnatin jihar ta tsara ta hanyar ceto gidajen da aka sake ginawa daga barazanar ambaliyar ruwa.”

A cewarsa, a cikin shekaru uku da suka gabata an fuskanci  barazanar ambaliyar ruwa a cikin al’ummomin da aka sake tsugunar da su, “dole ne mu gina magudanan ruwa domin gujewa sake afkuwar irin wannan ambaliyar nan gaba.

“Har ila yau, yana da mahimmanci a gina magudanan ruwa da wuri don shawo kan afkuwar hakan nan gaba,” in ji Buni.

Shugabar tawagar ta Bankin Duniya, Misis Joy Iyanga Agene, ta ba da tabbacin bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin ceto al’umma daga ambaliyar ruwa.

Ta yaba wa gwamnatin Jihar Yobe bisa samar da yanayi mai kyau wanda ya inganta ayyukan da shirin na Acresal na Bankin Duniya a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa tawagar ta samu jagorancin Mista Vijay Kumar na Bankin Duniya, Joy Iyanga Agene, shugabar kungiyar Acresal, da Cesena Cabecchi, babbar kwararriya kan harkokin jin daɗin jama’a kuma kodinetan Bankin Duniya na Arewa, da Shehu Mohammed kodinetan Shirin Acresal a Jihar Yobe.

Leave a Reply