Ambaliyar ruwa ta rushe gidaje da dama a garin Zakirai da ke Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Aƙalla sama da gidaje 100 ne ambaliyar ruwa ta ruguje a garin Zakirai dake ƙaramar hukumar Gabasawa a garin Kano bayan ruwan sama mai ƙarfi, kamar yadda al’ummar garin suka bayyana.
KU KUMA KARANTA: KMT ya ba da tallafin Naira miliyan 1 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Gulani
Ambaliyar ta shafi layin dogo da kasuwar garin, sakamakon magudanan ruwa da suke zargi marasa inganci da aka gina a aikin titin da ake yi.
Har ila yau wasu mazauna garin na Zakirai sun bar gidajensu, yayin da wasu ke zaune a cikin ruwa.









