Ambaliyar ruwa ta kawo gagarumin tsaiko a sufurin jiragen sama a Dubai

0
172

Babban filin jiragen saman Dubai ya sauya akalar jirage da ke shirin sauka sakamakon mamakon ruwan saman da ya janyo ambaliya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Filin jiragen sama mafi yawan hada-hada a duniya ya dakatar da saukar jiragen sama da karfe 7:26 na yammacin Talata, amma ya sanar da dawo da ayyukansa bayan sama da awanni biyu.

Birnin Dubai, Cibiyar kasuwancin ta Gabas ta Tsakiya, ya fuskanci tsaiko sakamakon mamakon ruwan saman da ya janyo ambaliya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain, inda ya kai ga mutuwar mutum 18 a Oman ranar Lahadi.

Da rana an dakatar da ayyuka a filin jiragen saman na tsawon mintuna 25. Bidiyoyin da aka riƙa wallafawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jirage suke tafiya a filin jiragen sama wanda ruwa ya malale.

KU KUMA KARANTA: Afirka ta Kudu na cikin shirin ko-ta-kwana game da ambaliyar ruwa

Da yamma jiragen da ke tashi sun ci gaba da aiki, amma su ma sun fuskanci tsaiko. Hanyoyin da ke kai wa ga filin jiragen saman sun cika makil da ruwa.

An fuskanci irin wannan ibti’ai a sauran sassan Dubai da ma wasu yankunan kasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa mai arzikin mai a yankin Gulf.

Friederike Otto, jagoran masu duba yanayi da sauyin yanayi, ya ce dumamar yanayi ce ta haifar da ambaliyar ruwan.

“Akwai ayyukan da mutane suke yi na gurbata yanayi ne suka janyo ambaliyar ruwa a kasar Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa,” in ji Otto, jami’i a Cibiyar Grantham Mai Ayyuka Kan Sauyin Yanayi da ke Kwalejin Imperial.

Hotuna da bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda manyan kantuna a Dubai Mall da Mall of the Emirates suka fuskanci ambaliyar ruwan. Wata tashar jiragen ƙasa ma da ke Dubai ta cika makil da ruwa.

Wasu hanyoyi sun lalace, ruwa ya malale unguwanni da dama inda mazaunansu suka yi korafi cewa ruwa ya rika tsiyaya ta rufin kwano, kofofi da taguna.

An rufe makarantu a faɗin ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Larabar nan bayan an yi hasashen samun guguwa mai karfi. Gwamnatin Dubai kuma ta kara wa’adin izinin aiki daga gida ga ma’aikatanta zuwa ranar Laraba.

Wasu yankunan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun samu zubar ruwan sama da yawan inshi 3.2 a awanni 24, wanda ya kusa kaiwa kusan adadin da aka yi tsammani a shekara.

“Hukumar Hasashen Yanayi ta bukaci jama’a su dauki matakan kariya sannan su nisanci yankunan da ake da ambaliya da taruwar ruwa”, in ji wata sanarwa da aka fitar ta shafin X.

Wannan yanayi ya sa an ɗage wasan kusa da naƙarshe na Gasar Zakarun Asiya ta kwallon ƙafa da aka shirya yi tsakanin ƙungiyar Al Ain ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Al Ahli ta Saudiyya da awanni 24.

Bahrain ma ta fuskanci ambaliyar ruwan tare da samun tsawa da walƙiya da tsakar dare.

Bayan guguwa ta afka wa Oman, ta kuma kutsa zuwa yankunan Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da wasu yankunan Qatar, inda ta jefa mutane da dama cikin tasku.

An gano gawar wani yaro a ranar Talata, wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutum 18, wasu biyu kuma sun aɓta, in ji jami’an ceto a wata sanarwa da suka bai wa kamfanin dillancin labarai na ƙasar.

Yara ‘yan makaranta tara da manya uku sun mutu a lokacin da ruwa ya yi awon gaba da motocin da suke ciki, in ji kamfanin dillancin labaran a ranar Lahadi.

Leave a Reply