Ambaliyar Ruwa: Mutane miliyan 1 sun shiga wani hali – Zulum

0
91
Ambaliyar Ruwa: Mutane miliyan 1 sun shiga wani hali - Zulum

Ambaliyar Ruwa: Mutane miliyan 1 sun shiga wani hali – Zulum

Daga Idris Umar, Zariya

Farfesa Babagana Umar Zulum, ya bayyana cewa mutane miliyan 1 ne suka tagayyara sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a jihar, wanda ya faru a ranar Talata.

Da yake ganawa da manema labarai yayin rabon tallafi ga ‘yan gudun hijira a sansanin Bukassi da ke Maiduguri, Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bayar da agajin gaggawa don daƙile annobar ambaliyar, musamman a garuruwan Maiduguri da Jere.

Ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da aka yi ba, sai dai kusan kashi ɗaya bisa huɗu na garin Maiduguri ya cika da ruwa.

Zulum ya ce, “Abin da muke yi a safiyar yau shi ne samar da agajin gaggawa ga mutanen da ambaliyar ta shafa, wanda ya kunshi rabon abinci da wasu kayayyakin tallafi.”

KU KUMA KARANTA: Za a fuskanci ɓarkewar kwalara, rashin abinci da tsaro a Maiduguri – MƊD

Har ila yau, ya bayyana cewa tawagar bincike da ceto ta fara aikin tantance adadin mutanen da ambaliyar ta shafa da asarar dukiyoyi.

Ya ƙara da cewa bayanan za a tattara su don yin nazari da shirin taimakawa mutanen da abin ya shafa.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 3 don shawo kan matsalar ambaliyar, kuma za a yi amfani da kuɗin wajen magance ƙalubalen da ambaliyar Ruwa ya haifar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here