Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta shafe wasu sassan garin (Bidiyo)

0
119
Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta shafe wasu sassan garin (Bidiyo)

Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta shafe wasu sassan garin (Bidiyo)

Dubban mutane ne suka yi hijira daga gidajensu a wasu sassan Maiduguri a Jihar Borno sakamakon ambaliyar ruwa.

Bidiyoyin da suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya shanye tituna, mutane na guduwa domin neman mafaka.

Dubban jama’a sun kwana a waje sakamakon yadda ambaliyar ta shanye musu gidaje.

Ambaliyar wadda ta soma tun a makon da ya gabata, ta yi ƙamari a ranar Litinin da dare, inda aka wayi garin Talata mutane da dama sun shiga cikin wani hali.

Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta faru ne sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alao da ke ƙaramar hukumar Konduga a Jihar Borno.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 20, ta raba dubu 3 da muhallansu a Yobe

Tun a ranar Litinin gwamnatin ta Borno ta umarci a rufe makarantu a jihar sakamakon take-taken da gwamnatin jihar ta gani na yiwuwar samun ambaliyar ruwan.

Sassan Najeriya na ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu, wanda dama tuni hukumar hasashen yanayi ta ƙasar ta yi hasashen samun wannan ambaliya.

Ɗaruruwan mutane ne hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayar da rahoton sun rasu a ƙasar sakamakon ambaliyar ruwan, jihohin Bauchi da Sokoto da Zamfara da Jigawa na daga cikin jihohin da ambaliya ta fi yi wa ɓarna a ƙasar.

Kalli bidiyon a nan:

https://www.facebook.com/Neptunehausa/videos/1090825312746108/

Leave a Reply