Ambaliyar ruwa a Arewa ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli – NEMA

0
94
Ambaliyar ruwa a Arewa ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli - NEMA

Ambaliyar ruwa a Arewa ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli – NEMA

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta bayar da rahoton cewar mutum 49 ne suka rasu, yayin da dubbai suka rasa muhallinsu, sakamakon ambaliyar ruwa a Arewa Maso Gabas.

Jihohi uku a Arewa Maso Gabas, da suka haɗa da Jigawa da Adamawa da Taraba, ambaliyar ruwa ta mamaye su, inda mutum 41,344 suka rasa matsugunansu, in ji kakakin hukumar NEMA, Manzo Ezekiel.

A 2022, Najeriya ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni cikin sama da shekaru 10, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 600, tare da raba kusan miliyan 1.4 da muhallansu tare da lalata kadada 440,000 na gonaki.

“Muna shiga kakar damina tsundum, musamman a Arewacin ƙasar kuma lamarin yana da matuƙar muni,” in ji Ezekiel.

Ambaliyar ta kuma lalata gonaki kusan hekta 693.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa a Sudan ya kashe fiye da mutum 130
Najeriya dai na fama da hauhawar farashi, wanda hakan ya haifar da tashin farashin kayan masarufi.

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya ƙara haifar da matsaloli a fannin noma, inda manoma ke barin gonakinsu a yankin Arewa Maso Gabas sakamakon hare-haren ’yan bindiga ke kaiwa.

Gwamnati a hasashen ambaliyar ruwa na bana, ta ce 31 daga cikin jihohin ƙasar nan 36 na cikin hatsarin fuskantar yawan ambaliyar ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here