No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ambaliya ta yi ɓarna a jihohi 20, wasu 13 na cikin haɗari

Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa, ƙananan hukumomi 52 a jihohi 20 ne ambaliya ta shafa.

Darakta-Janar na Hukumar, Zubaida Umar, ta ce akwai yiwuwar ƙaruwar adadin jihohin da abin ya shafa zuwa 33 tsakanin watan Agusta zuwa Oktoba, bisa hasashen da Hukumar Kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi.

Da take magana a wani taron agajin gaggawa ta kasa a Abuja, Zubaida ta ce, kawo yanzu ambaliyar ta yi ajalin mutane uku.

Ta danganta raguwar adadin mace-macen da ake samu sda karuwar wayar da kan al’umma kan hanyoyin kauce wa mutuwa da hadari a lokacin ambaliya.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano – SEMA

Dangane da sauya wa jama’a matsuguni daga wurare masu ambaliya, ta ce a jihohin Kebbi da Sokkwato, gwamnati ta yi nasarar sauya wa mutane wurin  zama zuwa kan tudu.

Ta kuma jaddada cewa an shawarci gwamnatocin jihohi da su ci gaba da tsugunar da jama’a a wuraren da suka fi aminci.

Zubaida Umar ta jaddada cewa hukumar NEMA ta sauya salon aikinta zuwa na kariya daga aukuwar abin da ake gudu, maimakon bari sai ya faru kafin a ɗauki mataki.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...