Alƙawura 5 da Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da ’yan Hisbah

0
144

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar cewa za ta yi wa jami’anta karin albashi domin su ji dadin gudanar da ayyukansu.

Shugubanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya kara da aikin hukumar na ‘Operation Kau Da Baɗala’ zai ci gaba gadan-gadan, babu kama hannun yaro.

Sheikh Daurawa wanda ya dawo aiki ranar Talata, ya sanar cewa hakan na daga cikin alkaruwa biyar da gwamnan jihar Abba Kabir, ya yi wa hukumar kamar haka:

1- Samar da motocin aiki ga rundunar Operation Kau Da Badala da kuma bunkasa shirin hukumar na ‘taya ni mu gyara’, wanda ya mayar da hankali kan ƙananan ’yan mata.

2- “Za a ƙara wa ’yan Hisbah Albashi. Shekara 20 da suka wuce albashin N10,000 ne, waɗanda ke hedikwata kuma N15,000.”

3- Samar wa Hisbah kayan aiki.

4- Daina korar jami’an Hisbah saboda siyasa.

5- Kafa makarantar koyar da a ikin Hisbah a aikace.

KU KUMA KARANTA: An yi sulhu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Daurawa

Malamin ya ba wa masu aikata baɗala a Jihar Kano wa’adin mako biyu su tuba, ko su gamu da fushin rundunar ‘Operation Kau Da Baɗala’.

Shugaban hisban ya ce, hukumar ta tanadi fom mai suna ‘na tuba na daina’, wanda duk wanda ke son daina baɗala zai je ya cike domin gwamnati ta sama masa abin da zai inganta rayuwarsa a ɓangaren sana’a ko neman ilimi.

A cewarsa, duk wanda ya kawo kansa Hisha ya cika fom, za “a kai wa mai girma gwamna ya taimaka masa da sana’a da jari, wanda zai koma makaranta a taimaka masa komawa makaranta, mun buɗe wannan kofa daga nan har zuwa mako biyu.”

Sai dai ya yi ƙarin haske da cewa kofar tuba da hukumar ta buɗe ba ya nufin za a bar kowa ya yi abin da ya ga dama.

An buɗe damar ce domin wanda ke aikata laifi ya gabatar da kansa hukumar ta san ya daina ta kuma dauki bayanansa domin ganin gwamnati ta yi abin da ya dace.

“Idan wannan lokaci ya wuce mutum bai zo ya tuba ba, to shi ke nan, Operation Kau Da Baɗala,…”

Leave a Reply