Daga Ibraheem El-Tafseer
Kamar yadda hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana cewa, jihar Yobe tana ɗaya daga cikin jihohin da ke fuskantar ambaliyar ruwa a daminar bana. Wannan ne ya sa al’ummar garin Nguru da ke jihar Yobe, musamman unguwannin da suke fuskantar ambaliyar ruwa duk shekara, suka katange unguwannin nasu daga fuskantar ambaliyar ruwa. Wato suka tona ƙaton rami mai zurfi, kamar kwalbati, yadda ko da ruwan ya zo ba zai iya haura wa ba, sai dai ya bi ta wannan ramin ya tafi.
Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata, unguwar Barma da ke cikin garin na Nguru, inda ambaliyar ruwa ya rushe kusan dukkan gidajen da ke unguwar da gonakinsu da kuma wuraren sana’o’insu. Wanda hakan ya haifar da da yawa suka rasa muhallansu, dole sai da wasu suka yi ƙaura suka bar unguwar.
KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Bauchi ta gina sansanonin ‘yan gudun hijira
Wani mazaunin unguwar mai suna Hamza Sulaiman, ya shaida wa manema labarai cewa, “a shekarar da ta gabata mun fuskanci ambaliyar ruwa a wannan unguwa, gidaje da yawa sun rushe gaba ɗaya, ko ɗaki ɗaya bai saura ba. Akwai gidajen da masu gidajen sun gagara tayar da ko ɗaki ɗaya, saboda yanayin halin rayuwa da ake fama da shi” inji shi.
Wasu zaratan matasa ne tare da taimkon ƙaramar hukumar Nguru, suka duƙufa wurin katange unguwannin da ambaliyar ruwan ke yiwa barazana. Ɗaya daga cikin matasan mai suna Mohammed Abubakar ya shaida wa Wakilinmu cewa “ambaliyar ruwan tana damun mu duk shekara a wannan unguwa, wasu ba sa iya kwana a gidajensu, dole sai sun fita sun bar gidajen nasu, saboda ruwan ya cinye gidajen. Shi ya sa muke wannan aiki don kare kanmu daga barazanar ambaliyar ruwa da muke fuskanta”. inji shi
Shugaban ƙaramar hukumar Nguru, Alhaji Madu Kachalla ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta gyara magudanan ruwa, sannan an kwashe dattin da ke ciki domin gudun aukuwar ambaliyar ruwan. Sannan ana ci gaba da katange unguwannin da ambaliyar ruwa ke yiwa barazana. Sannan akwai wuraren da ruwa ke taru wa (Kogi), za mu sa a yashe ruwan gaba ɗaya. Idan ba a yashe ruwan ba, idan ruwan saman ya zo, shi ne yake haifar da ambaliyar”. inji Madu Kachalla.