Al’ummar Kano ku rungumi zaman lafiya, domin hakan shi ne nasara – Sarkin Kano Sanusi II
Daga Ibraheem El-Tafseer
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll,ya yi ƙira ga al’ummar jihar Kano da su kasance masu bin doka da oda, su zauna lafiya, kuma su haɗa kai don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa da ya ke jawabi a wurin taron buɗe-baki na musamman a fadarsa a ranar Lahadi, Sarkin ya soki masu adawa da dawowarsa kan karagar mulki, inda ya bayyana cewa “wuta za ta cinye masu tayar da zaune tsaye a cikin birnin Kano.”
Sanusi ya kara da cewa, waɗanda ke kalubalantar sarautarsa na jayaiya ne da ikon Allah, inda ya ce za su “fuskanci sakamako mai muni a ƙarshe domin sun bijirewa abin da Allah Ya ƙaddara.”
“Muna roƙon kowa ya kasance cikin lumana. Wannan lamari ne na nufin Allah, kuma Shi ba Ya bukatar taimakon kowa,” in ji Sarkin cikin harshen Hausa a wani bidiyo da TheCable ta gani.
KU KUMA KARANTA:Wajibi ne gwamnatin Kano ta bi hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan Sarkin Kano – Sarkin Dawaki Babba
“Muyi hakuri mu ci gaba da yin addu’a, domin Allah na tare da waɗanda ke kan hanya madaidaiciya.
“Wuta za ta cinye duk wanda ke son haddasa fitina a Kano. Allah Ya kare mu da al’ummarmu daga dukkan sharri. Mu ci gaba da zaman lafiya da kuma yin addu’a.
“Wanda ya ƙalubalanci hukuncin Allah ba zai taɓa cin nasara ba.”
Jawaban Sanusi sun biyo bayan umarnin Gwamnan Kano, Abba Yusuf, na cewa majalisun masarautu su fara shirin Hawan Sallah.
Bayan haka, Aminu Ado Bayero, tuɓaɓɓen Sarkin Kano, shi ma ya sanar da hukumomin tsaro shirinsa na gudanar da Hawan da kuma bikin cika shekaru biyar a matsayin Sarkin Kano.









