Al’ummar garin ‘Yanshana a Kano sun koka kan matsalar rashin ruwa da wuta
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Al’ummar yankin garin ‘Yanshana dake Cikin karamar hukumar Kumbotso sun koka akan matsalar rashin Hanya, Asibiti, Wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa.
Inda Sukace sama da shekara 3 da rabi suke fama da matsalar rashin wutar lantarki wadda transfomar su ta lalace har yanzu ba’a samu wanda zai gyara musu ba.
Sunce, sun kai koke wajen wakilan su na Majalisar dokokin Kano dana Tarayya harma da Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso amma shiru kake ji.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta tabbatar da tattara Miliyan 15 ga ƙananan hukumomi 44 domin sayawa Sarkin Kano mota
Sun kara cewar, yanzu haka sun rubuta takardun neman dauki ga ma’aikatun da lamarin ya shafa har zuwa ofishin Gwamnan Kano amma har yanzu Babu amo ba labari.
Suma Direbobin Baburin Adaidaita sahu da suke jigilar jama’a musamman ma’aikatan gwamnati da Daliban sakandare dana Sa’adatu Rimi sun bayyana rashin Jin dadin su dangane da matsalar rashin kyawun hanya a ‘yanshana.
Daga nan su kai kira ga Gwamnan Kano ya kai musu dauki na Gaggawa sakamakon yanayin Damuna da take tunkarowa ga matsalar rashin kyawun hanya da Asibitin yankin.









