Daga Ibraheem El-Tafseer
‘Yan’uwa musulmi na Harka Islamiyya ƙarƙashin jagorancin Shaikh Zakzaky, waɗanda aka fi sani Shi’a, sun yi wa hukumar ‘yansandan Najeriya martani kan wata takarda da suka fitar. Martanin wanda Farfesa I. H. Mshelgeru ya sa wa hanu ta fara da cewa “mun ci karo da wani saƙo daga Hukumar ‘ynsanda ta jihar Borno cewa wai Harkar Musulunci a Nijeriya na ƙoƙarin shirya abin da su ka ƙira ramuwar gayya kan zargin kisan mabiya Harkar da ‘yansanda su ka yi a Kaduna.
Saƙon mai lamaba CB:0900/BRS/VOL.12/60 ɗauke da kwanan watan 9 ga Afrilu, 2024, ya ƙunshi wani abu wai shi gargaɗi da aka aika zuwa dukkan ofisoshin ‘yansanda na jihar, kan cewa wai “ɓangaren soji” na Harka na shirya kai wa ‘yansanda farmaki a wurare kamar otal otal, wuraren shaƙatawa, gidaje da sauran su.
Haƙiƙa muna masu watsi da wannan labarin ƙaryar a yayin da kuma muke matuƙar mamakin ko mece ce manufar da ke tattare da wannan makircin.
Muna sanar da jama’a cewa, wannan ƙirƙirarren karya ne da ba ya da wani tushe.
KU KUMA KARANTA:Bukin Sallah: El-Zakzaky Ya Raba Buhunan Hatsi, Da Tsabar Kudi Ga ’Yan Jarida Na Kaduna
A haƙiƙa ma, ya saɓa wa dukkan hankali da tunani, wai a ce jihar da aka aikata kashe-kashe daban, amma jihar da ake gargaɗin ɗaukar fansa kuma daban, alhali akwai bambancin kusan kilomita 800 a tsakani.
Haka kuma, ba hankali a ce gamayyar jami’an tsaron rundunar ‘yansanda ta kai ma mutum hari a rana tsaka, amma kuma sai ya ɗauki fansa kan wasu ‘yan tsiraru da ke aiki a otal-otal da wuraren shaƙatawa.
Sanannen abu ne cewa, a sama da shekara 40 da Sheikh Zakzaky ya kwashe yana ƙira, Harkar Musulunci nan ba ta taɓa aiwatar da wani abu wai shi ramuwar gayya ba, walau a kan jami’an tsaro ko zauna gari banzan da akan turo , alhali ba irin muzgunawa da tunzurawar da ba ai mana ba.
Saboda haka al’umma su sani idan har aka yi wata ta’asa a wuraren da jami’an tsaron suka ambata, to lalle ba Harkar Musulunci ba ne.
Ga alama su da suka kai hari kan masu muzaharar lumana su ne kuma ke shirin yin wata mummunar ta’asar a kan abokan aikinsu da ‘yan ƙasa da ba su ji ba su gani.
Bugu da ƙari, muna kira ga Hukumar ‘yansanda da ta gaggauta janye wannan bayani nata. Abin dariya ma ne a ce wai Harkar Musulunci na da ɓangaren soji masu makami, alhalin duk duniya ta san haƙiƙar masu makamin wanda su ka zaɓi kashe mata da ƙananan yara, maimakon gadan-gadan su fuskanci ‘yan fashin daji da kidnafin da sauran ta’addancin da ke watayawa a ƙasa.
Muna masu amfani da wannan damar kuma domin ɗora alhakin mummunan hari kan masu muzaharar Quds a Kaduna da Zariya a makon da ya gabata, a kan Gwamnatin Tarayya da Jihar Kaduna. Za kuma mu ci gaba da bin matakan duk da suka dace don ganin cewa wannan ɗanyen aikin bai tafi a banza ba.
A karshe, muna ƙira da babbar murya cewa, kar fa a ɗauki shirun mu da kamewar mu na tsawon lokaci a banza, domin hankali ma na hukunta cewa akwai ƙarshe ga kowane irin shisshigi da wuce gona da iri.
Sheikh Zakzaky (H) ya faɗa kuma ya sha jaddadawa cewa ranar ramuwa tana nan tafe, kuma tabbas ba makawa za ta zo.
Ba wanda ya isa yai amfani da wani gargaɗin ƙarya ko shirme ya tunzura mu, ko ya yi mana ingiza mai kantu ruwa. Sai dai tabbas akwai ranar ƙin dillanci.