No menu items!

Sample Page Title

Date:

Albashin direbobina ya ninka mafi ƙarancin albashi a Najeriya sau 4 – Ɗangote

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban kamfanin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote, ya bayyana cewa har yanzu ana yiwa matatar man sa mummunar makarkashiya daga wasu manyan ƴan kasuwa da ke harkar man fetur.

Ana Kuma hakan ne da nufin dakile nasarar matatar da a yanzu, ta fi kowacce girma a nahiyar Afirka.

Dangote ya yi wannan zargin ne a yayin bikin cika shekara daya da matatar ta fara fitar da man fetur zuwa kasuwanni.

“Wasu manyan masu ruwa da tsaki a harkar mai na ƙasa da waje na kokarin ganin matatar da ta kai darajar dala biliyan 20 ba ta samu nasara ba”.

KU KUMA KARANTA: Matatar Ɗangote ta fitar da motoci 1,000 don fara rarraba man fetur kai tsaye ga jihohin Najeriya

“Tun daga watan Yunin 2025 zuwa yanzu, matatar ta fitar da lita biliyan 1 da miliyan 800 na man fetur zuwa kasuwannin waje, kuma tana da damar biyan bukatun cikin gida”. In ji shi.

Ya Kuma kara da cewa, tun daga lokacin da aka kammala aikin matatar a watan Satumbar 2024, Najeriya ta fara ganin karancin dogayen layukan neman fetur da suka dade suna addabar ƴan ƙasa fiye da shekaru 50.

Sannan ya ce, sabbin motocin CNG 4,000 da ya shigo da su, za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...