Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

0
98
Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi - TUC/NLC

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauƙo Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadagon ta TUC Komared Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar ƙolinmu, tayin da shugaban ƙasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 ɗin nan da babu ne gara ba daɗi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauƙin shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun miƙa wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.

Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matuƙar gwamnati ba ta farka ta ɗauki matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan ƙwadagon sun yaɗa gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Leave a Reply