Alarammomi sun buƙaci Gwamnatin Kano da ta bawa tsangayu kulawa

0
263
Alarammomi sun buƙaci Gwamnatin Kano da ta bawa tsangayu kulawa

Alarammomi sun buƙaci Gwamnatin Kano da ta bawa tsangayu kulawa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Alarammomi da malamai masu kula da tsangayun Alƙur’ani a jihar Kano sun nemi Gwamnatin Kano ta tabbatar da kulawa ta musamman ga tsangayun karatun Alkur’ani a faɗin jihar.

Wannan na cikin sanarwar da Kungiyar Tsangaya Abar Alfaharinmu ta fitar mai dauke da sa hannu Shuagbanta Alaramma Muhammad Sani Musa Nuhu (Sanin Malam).

Ya ce, suna neman a saka wakilin tsangayu a cikin Majalisar Koli ta Malamai da aka kafa, a samar da fitulun sola a dukkan tsangayu, a dinga ware musu kaso a kasafin kudin kowace shekara, da kuma gina rumfunan karatu, bandakuna da dakunan kwana ga almajirai.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya karrama zakarun gasar karatun Alƙur’ani, ya ba su kujerun aikin Hajji

Sauran bukatun sun hada da samar da ruwan sha, muhalli na dindindin, karrama fitattun alarammomi, sanya almajirai cikin shirye-shiryen koyon sana’a da raba jari da kuma samun kaso a tallafin takin zamani.

Sanarwar ta kuma yi godiya ga Gwamnan kan nadin Gwani Musa Falaki a matsayin mai taimakawa gwamna kan harkar tsangayu, tare da jinjina wa tsohon Gwamna Kwankwaso bisa ɗaukar nauyin koyar da almajirai kyauta.

Leave a Reply