Al-Burhan ya ce ba zai sasanta da rundunar RSF ta Sudan ba

0
129

Shugaban Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya sha alwashin ci gaba da yaƙin da suke yi da rundunar RSF a ƙasar, inda ya yi watsi da buƙatar tsagaita wuta ta baya-bayan nan.

A farkon makon nan ne Shugaban RSF Hamdan Dagalo ya amince da buƙatar tsagaita wuta wadda ƙungiyoyin farar hula suka gabatar, wanda hakan ya ƙunshi idan sojoji sun amince.

Sai dai masu lura da al’amura sun mayar da martani cikin kakkausar murya bisa la’akari da alƙawurran da rundunar ta yi a baya da ba ta cika ba.

Ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da dama a farkon watannin yaƙin. Sai dai masu ido sun mayar da martani cikin kakkausar murya bisa la’akari da alƙawurran da rundunar ta yi a baya waɗanda ba ta cika ba.

Ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da dama waɗanda ba su ɗore ba a farkon watannin yaƙin.

KU KUMA KARANTA: Sudan ta kori ma’aikatan jakadancin Chadi daga Khartoum

“Duka duniya ta shaida yadda dakarun ‘yan tawayen nan suka rinka aikata laifukan yaƙi da kuma laifin take hakkin bil adama a Yammacin Darfur da sauran yankunan Sudan.

Sakamakon haka, ba za mu sasanta da su ba, ba mu da wata yarjejeniya da su,” kamar yadda Burhan ya bayyana, wanda shi ne shugaban na Sudan a lokacin da dakarunsa suka taru a birnin Port Sudan.

An soma wannan yakin a ranar 15 ga watan Afrilu inda ya lalata wurare masu yawa a Sudan da kuma raba da sama da mutum miliyan 7.5 da muhallansu.

Ganin cewa RSF ta samu dama a wannan yaƙin, Ƙungiyar Intergovernmental Authority on Development, ta samu Burhan da Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, a watan da ya gabata, don amincewa da wani taron kai tsaye.

Sai dai Burhan a ranar Juma’a ya yi watsi da hakan inda ya ƙira abokin adawar tasa a matsayin “sakarai”, kuma “matsoraci”.

Ya yi watsi da buƙatar tsagaita wuta da Dagalo ya saka wa hannu a Addis Ababa babban birnin Habasha a wannan makon.

Haka kuma Burhan ya caccaki shugabannin Afirka waɗanda suka haɗa da Habasha da Kenya waɗanda suka karɓi Dagalo a wata ziyara da ya kai a makon nan da kuma wasu ‘yan siyasar Sudan waɗanda suka haɗu da shi a Habasha.

Leave a Reply