Gwamnatin Tarayya ta ce ba abu ne mai sauƙi ba wajen zartar da wasu daga cikin bukatun Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC da aka suka cimma a watan Oktoban 2023 a lokaci guda ba.
Ƙaramar Ministar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce, ta bayyana haka a ranar Juma’a.
Ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin yarjejeniyar da aka ƙulla da ke neman a samar da cibiyoyin sauya motoci zuwa masu amfani da iskar gas zai ɗauki lokaci kafin cibiyoyin su wadata ko ina.
Kazalika ta ce kwamitin da ke kula da samar da cibiyoyin yana aiki tuƙuru, don ganin an cika wannan alƙawari da aka ɗaukar wa NLC a shekarar da ta gabata.
KU KUMA KARANTA: Ranar Ma’aikata: NLC Ta Buƙaci Ma’aikata Da Shiga Harkokin Siyasa Dumu-Dumu A Dama Da Su
A watan Oktoban bara ne dai, Gwamnatin Tarayya da NLC suka cimma jerin yarjejeniyoyi da suka kunshi rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin talauci da fatara biyo bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi.
Sauran bukatun sun haɗa da ɗaga darajar naira da tashin farashi da kuma matsalar tsaro da dai sauransu.
Ƙungiyar Ƙwadago dai ta bai wa gwamnati wa’adin mako biyu da ta cika alƙawuran da ta ɗaukar mata ko ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Hakan dai ya biyo bayan koke-koke da zanga-zanga da wasu ‘yan Najeriya suka gudanar a makon nan kan tashin gwauron zaɓi da kayan masarufi ke yi.