Akwai yiwuwar masu amfani da shafin X su fara biyan kuɗi

0
307

Mai kamfanin sada zumunta na dandalin X wanda a baya ake ƙira da Twitter, Elon Musk, ya ce masu amfani da shafin ka iya fara biyan kuɗi domin amfani da shi.

Attajirin mai kuɗin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci wani zauren tattaunawa da firaministan Isra’ila, Benyamin Netanyahu a jihar California.

Wakiliyar BBC ta ce Musk ya ce a halin yanzu masu amfani da shafin X za su ci gaba da cin ɓagas, amma nan gaba batun biya zai ɓullo.

KU KUMA KARANTA: Zan sauya wa Twitter sabon tambari – Elon Musk

Tun bayan da ya karɓi ikon da kamfanin dai ya ke ta ƙoƙarin fito da sabbin matakai da ba ya yi wa ma’aikata da masu amfani da shafin daɗi.

Matakin biyan kuɗin da alama zai rage wa X mabiya da kuma samun raguwar masu tallace-tallace a ciki.

Leave a Reply