Hukumar tsaro ta farin kaya, (SSS), a ranar Alhamis a Abuja, ta gargaɗi jama’a da su yi taka-tsan-tsan da hare-haren ‘yan ta’adda a yayin da suke tsaka da bikin Eid-el-Kabir.
Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ya bayyana cewa, rahotannin da suka zo mata na nuni da shirin kai hari kan wuraren ibada da wuraren shaƙatawa kafin da kuma lokacin bukukuwan na sallah.
A cewarsa, rahotannin sun tabbatar da ƙwato wasu bama-bamai da ake zargin ‘yan ta’adda ne da aka yi a yayin wani aikin haɗin gwiwa da sashen da jami’an tsaron ‘yan uwanta suka yi.
KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta karrama limamin da ya tausaya wa kyanwar da ta hau kansa a sahun sallah
Ya kuma bayyana cewa, sashen ya kai samame a maɓoyar ‘yan ta’adda a jihohin Kogi da Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata tare da haɗin gwiwar rundunar sojojin Nijeriya da rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Mista Afunanya ya ƙara da cewa, samamen da aka kai kan titin Abuja zuwa Keffi a ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa ya kai ga kama wani da ake zargin ɗan bindiga ne.
Ya bayyana cewa an samu nasarar ƙwato harsasai 486 na alburusai mai girman 7.62 x39mm, IEDs 22, N31,500 da kuma mota ƙirar Volkswagen Golf guda ɗaya mai lamba RBC202XA yayin aikin.
Ya kuma bayyana cewa rundunar haɗin guiwar jami’an tsaron sun kai samame maɓoyar wani ɗan fashin gidan yari kuma fitaccen shugaban ‘yan daba a Ejule a ƙaramar hukumar Ofu a jihar Kogi ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa, ‘yan ƙungiyar da ake zargin sun haɗa da sojoji ne a wani fafatawar da aka yi da bindiga kuma an kashe shugaban ƙungiyar yayin da wasu suka gudu, in ji shi.
Mista Afunanya ya kuma bayyana cewa, kayayyakin da aka ƙwato a wurin sun haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya ɗauke da mujallu uku cikakku, makamai na gida guda shida, wayoyi biyu da kuma layu.
Ya kuma umarci ma’aikata da masu kula da wuraren taruwar jama’a da suka haɗa da kasuwanni da kantuna da su kasance cikin shiri da kuma kai rahoton duk wani motsi da mutane da ke da shakku ga hukumomin tsaro da abin ya shafa.
Mista Afunanya ya ba da tabbacin cewa SSS za ta ci gaba da haɗa gwiwa da ‘yan uwa jami’an tsaro don gudanar da atisayen da suka dace don daƙile masu aikata laifuka da ayyukansu.
[…] KU KUMA KARANTA: Akwai yiwuwar akai hare-hare a lokacin bukukuwan Sallah – SSS […]
[…] KU KUMA KARANTA: Akwai yiwuwar akai hare-hare a lokacin bukukuwan Sallah – SSS […]