Daga Ibraheem El-Tafseer
Hukumar tsaron farin kaya ta ‘yan sandan ciki ta Najeria, (DSS) ta bayyana cewa akwai wasu da suke shirin tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan miƙa mulki da za a yi a wasu jihohin ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce mutanen suna son yi wa aikin jami’an tsaro naƙasu ne tare kuma da tayar da hankalin jama’a su jefa tsoro ga ‘yan ƙasar a lokacin.
A sanarwar wadda kakakinta, Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta buƙaci jama’a da ‘yan jarida da ‘yan ƙungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar da su bi ƙa’idojin da aka tsara a lokacin bikin a ko’ina a faɗin ƙasar.
Haka kuma sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya ko na ƙanzon-kurege da na zuzuta al’amura da kuma duk wani abu na neman razanarwa.
KU KUMA KARANTA: DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta
Hukumar ta kuma shawarci duk wani mutum da ba shi da takardar izini ko ta tantancewa da ya kauce wa shiga wasu wuraren a lokacin da ake bikin.
DSS ta bai wa jama’a tabbacin ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a ko’ina a faɗin ƙasar.
A ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu 2023 ne za a yi bikin miƙa mulki da rantsar da sabon shugaban ƙasa a Abuja da kuma gwamnoni a wasu jihohin Najeriyar.