Akpabio ya buƙaci Tinubu ya hana ministoci tafiya ƙasashen ƙetare

0
190

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanyawa ministocinsa takunkumin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare lokacin da ake kare kasafin kuɗin ma’aikatu.

Akpabio yace irin waɗannan tafiye-tafiye na hana ministocin da shugabannin hukumomin gwamnati bayyana a gaban ‘yan majalisu domin ƙare kasafin kuɗin da suka gabatar da kuma tuhumar da majalisa ke yi a kan wasu ayyukan da ake sakawa.

Shugaban majalisar ya yi alƙawarin cewar zasu bincike kasafin da shugaban ƙasar ya gabatar sosai, kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu dama, kafin amincewa da shi.

Akpabio ya kuma buƙaci ɓangaren zartarwar da ya nemo hanyar rage basussukan da ake bin Najeriya, duk da yake sun san cewar wannan gwamnati ta gaji wasu basussukan daga gwamnatin da ta gabace ta.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024

Shugaban majalisar ya yi kuma alƙawarin haɗa kai da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin daƙile hanyoyin da jami’an gwamnati ke amfani da su suna karkata dukiyar jama’a.

Wannan shine kasafin kuɗi na farko da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar tun bayan hawansa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply