AJAG ta yi Allah-wadai da tsare ɗan jarida Nasiru Yelwa, ta buƙaci a gaggauta sake shi

0
308
AJAG ta yi Allah-wadai da tsare ɗan jarida Nasiru Yelwa, ta buƙaci a gaggauta sake shi
Ɗan jarida Nasiru Hassan Yelwa, wakilin gidan Talabijin na Iran Press

AJAG ta yi Allah-wadai da tsare ɗan jarida Nasiru Yelwa, ta buƙaci a gaggauta sake shi

Kungiyar ‘yan jarida ta Afrika da ke yaƙi da kisan ƙare dangi (AJAG) ta yi ƙira da a gaggauta sakin Nasiru Hassan Yelwa, ɗan jaridar IRAN PRESS, wanda aka kama a lokacin da yake ɗaukar labarin zagayen Mauludi a Abuja a ranar Laraba 10 ga Satumba, 2025.

A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, gamayyar manyan ‘yan jarida daga ƙasashen Afirka sama da 30 sun yi tir da kamun da aka yi masa, sun bayyana kamun a matsayin rashin adalci, tare da bayyana cewa Yalwa na gudanar da aikinsa na halal a lokacin da jami’an ‘yansandan Najeriya suka tsare shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “An kama Nasiru ne a yayin da yake gudanar da muhimmin aikin jarida, ci gaba da tsare shi ba tare da an tuhume shi da wani laifi ba, ba wai kawai ya saɓawa doka ba amma babban take haƙƙin ‘yan jarida ne.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta jaddada ƙudirin kare ‘yancin ‘yan jarida da ‘yancin faɗin albarkacin baki

AJAG ta bayyana cewa ƙoƙarin da Lauyoyin Yelwa suka yi na ganin an sake shi ya ci tura, saboda hukumomin ‘yansanda sun ƙi bayar da hujjar kama shi.

A cewar ƙungiyar, iyalan ɗan jaridar su ma sun buƙaci a yi musu bayani kan kamun, amma babu wani dalili a hukumance da ‘yan sandan suka bayar.

 

AJAG ta bayyana lamarin a matsayin wani harin da aka kai kan ƙimar dimokuraɗiyyar da ‘yancin aikin jarida, ƙungiyar ta AJAG ta yi gargaɗin cewa bai kamata a amince da kame da cin zarafin ‘yan jarida ba bisa ƙa’ida ba a kowace al’umma ta dimokuraɗiyya.

“Muna yin Allah wadai da duk wani abu na cin zarafi da cin mutuncin ‘yan jarida da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kare aikinsu, aikin jarida ba laifi ba ne,” in ji AJAG.

Ƙungiyar ta buƙaci rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta tabbatar da bin doka da oda tare da gaggauta sakin Nasiru Yalwa ba tare da ɓata lokaci ba.

Leave a Reply