Afirka ta Kudu ta shigar da ƙara don a ɗauki sabbin matakai a kan Isra’ila

0
170

Afirka ta Kudu ta shigar da wata buƙatar gaggawa ta neman a ɗauki ƙarin matakai da kuma yin kwaskwarima kan hukuncin da Kotun Duniya ta yanke a kan batun kisan ƙare-dangin da ake tuhumar Isra’ila da shi, kamar yadda Babbar Kotun Majalisar Ɗinkin Duniyar ta faɗa.

A cikin sabuwar buƙatar tata ta gaggawa, Afirka ta Kudu ta ce ta gabatar da ita ne saboda “sababbin bayanan gaskiya da suka ɓullo, da kuma sauye-sauyen da aka samu a halin da ake ciki a Gaza, musamman halin yunwa da ake fama da ita,” in ji wata sanarwa da Kotun Duniyar ICJ ta fitar.

A cewar buƙatar, waɗannan kashe-kashe da Isra’ila ke ci gaba da yi, sun saɓa wa yarjejeniyar kariya da hukunta laifukan kisan ƙare-dangi da kuma keta matakan wucin-gadi da wannan kotun ta bayar a watan Janairu.

Ana tuhumar Isra’ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya. Hukuncin wucin-gadi da aka yanke a watan Janairu ya umarci Tel Aviv ta dakatar da kisan ƙare-dangi tare da ɗaukar matakan tabbatar da cewa an ba da taimakon jinƙai ga fararen-hula a Gaza.

KU KUMA KARANTA: Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 30,534 yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare

Munanan hare-hare Isra’ila ta ƙaddamar da wani ƙazamin farmakin soji, wanda yanzu haka aka shiga kwana na 152 tana kai hare-hare a Zirin Gaza, tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda Tel Aviv ta ce ya kashe kusan mutum 1,200.

Fiye da Falasɗinawa 30,700 aka kashe tun daga lokacin, sannan sama da 72,000 suka jikkata, yayin da ake ta lalata ababen more rayuwa da kuma sanya al’ummar yankin Gaza a cikin halin yunwa.

Har ila yau Isra’ila ta ƙaƙaba wa Zirin Gaza wani shinge da takunkumai, waɗanda suka bar al’ummarta, musamman mazauna arewacin Gaza, cikin halin ha’ula’i.

Yakin Isra’ila ya sa kashi 85 cikin 100 na al’ummar Gaza sun yi gudun hijira a cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna, yayin da aka lalata kashi 60 na ababen more rayuwa na yankin, a cewar MƊD.

Leave a Reply