ADC ba za ta lamunci ƙaƙaba ‘yan takara ko cin amanar jam’iyya ba – David Mark

0
226
ADC ba za ta lamunci ƙaƙaba 'yan takara ko cin amanar jam’iyya ba - David Mark
Sanata David Mark

ADC ba za ta lamunci ƙaƙaba ‘yan takara ko cin amanar jam’iyya ba – David Mark

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban riƙon kwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta lamunci kakaba ‘yan takara , cin amanar jam’iyya ko rashin da’a ba a karkashin jagorancinsa.

A yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, David Mark ya sha alwashin jagorantar ADC da gaskiya, adalci da dimokuradiyya. Ya jinjinawa tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, bisa jajircewarsa da hidimar da ya yi.

KU KUMA KARANTA: Mambobin ADC sun shigar da ƙara akan sabbin shugabannin riƙo na jam’iyyar

Mark ya bayyana cewa jam’iyyar ta ware kashi 35 cikin 100 na mukaman shugabanci ga mata, tare da kudurin bai wa matasa ‘yan kasa da shekara 40 mukamai. Ya kuma bayyana cewa sabon shugabancin jam’iyyar na kasa zai sake duba kundin tsarin mulki da manufofin jam’iyyar domin su dace da bukatun ‘yan kasa.

Ya kara da cewa jam’iyyar za ta kafa kwamitin tsara manufofi mai mutum 50 da zai mayar da hankali kan fannoni irin su lafiya, ilimi, noma, fasaha, tsaro, da tattalin arziki. Mark ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara wa ADC baya, yana mai cewa ita ce jam’iyyar da ke bai wa kowa dama ba tare da nuna bambanci ba.

Leave a Reply