No menu items!

Sample Page Title

Date:

Adadin waɗanda suka rasu a fashewar tankar mai a Jihar Neja ya ƙaru

Adadin waɗanda suka rasu a sakamakon bindigar da tankar mai ta yi a Dikko Junction da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja a Jihar Neja ya kai 86, inda 55 suka jikkata kuma suke samun kulawa ta likitoci, kamar yadda hukumomin ƙasar suka tabbatar a ranar Lahadi.

Abdullahi Baba-Arah, wanda shi ne darakta janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, shi ne ya bayar da sabbin alƙaluman, inda ya ƙara da cewa akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su an binne su a cikin ƙabarin bai ɗaya.

“Jumullar mutum 86 ne aka tabbatar sun rasu, inda aka gano gawawwakinsu sannan aka binne su.

“An binne mutum 80 a cikin ƙabari guda na ɓai daya a harabar Dikko Pimary Healthcare Centre, biyar kuma iyalansu ne suka karɓe su domin su binne su, ɗaya kuma ya rasu a Dikko Pimary Healthcare Centre,” in ji Baba-Arah.

Tankar ta yi bindiga ne a daidai lokacin da mutanen wurin suka yi ƙoƙarin kwalfar man fetur ɗin cikinta da ke tsiyaya, lamarin da ya halaka waɗanda suka je ɗibar man.

KU KUMA KARANTA: Gobarar tankan mai ta yi ajalin mutuwar mutum 4

Ana yawan samun fashewar tankar mai bayan ta yi hatsari a Najeriya inda jama’a da dama da ke zuwa kwalfar man fetur ke mutuwa.

Ko a kwanakin baya sai da fiye da mutum 100 suka rasu a gobarar tankar mai a Jigawa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...