Adadin waɗanda suka mutu a tarzomar Kenya ya ƙaru
Ƙungiyar likitoci ta Kenya ta ce adadin waɗanda suka mutu, sanadiyar zanga-zangar ƙarin kuɗin haraji da gwamnatin ƙasar ta sanar, ya ƙaru zuwa 13.
Shugaban Ƙungiyar Simon Kigondu ne ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP adadin, a wata zantawa da suka yi da shi a yau Laraba.
Masu zanga-zangar waɗanda yawancinsu matasa ne, sun mamaye zauren majalisar dokokin kasar a jiya Talata, inda suka rinka jifar ‘yan sanda da duwatsu da kuma rushe shingen jami’an tsaro don kutsa kai cikin harabar majalisar.
Bayan faruwar lamarin, shugaban ƙasar William Ruto ya tura da jami’an soji don tarwatsa masu zanga-zangar.
KU KUMA KARANTA: Mutum 12 sun mutu a rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa a Chadi
Shugaba Ruto ya lashi takobin ɗaukar tsauraran matakai don tabbatar da zaman lafiya a ƙasar, inda ya sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.
Sai dai duk da ɗaukar wancan mataki, masu zanga-zangar sun ce babu gudu babu ja da baya game da ƙudirinsu na ci gaba da zanga-zangar, har sai haƙarsu ta cimma ruwa.
Wani jami’i a asibitin Kenyatta da ke birnin Nairobi, ya ce a asibitin kadai, jami’insu sun duba mutane 160 da suka samu raunukan harhasai wasu kuma kananan raunuka.
Ɗaya daga cikin abubuwan da masu zanga-zangar ke buƙata shi ne shugaban ƙasar William Ruto ya sauka daga muƙaminsa.
Matasan sun bayyana matakin gwamnatin Ruto na lafta wa jama’a haraji a matsayin wani sabon yunƙuri na jefa al’umma cikin ƙarin musiba, ganin yadda tuni matsalar tsadar rayuwa ta yi musu dabaibayi.