No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani bincike da ‘Mujallar The Lancet’ ta yi, ya nuna cewa, yawan al’ummomin kasashen duniya zai ci gaba da raguwa har zuwa karshen wannan ƙarni.

Binciken da kwararrun suka yi, ya yi ƙoƙarin hasashen adadin yawan al’ummar duniya baki daya, inda suke amfani da tarin alkaluman haife-haife da mace-mace da kuma abubuwan da ke haddasa ƙaruwar jama’a.

Binciken ya kuma yi gargadin cewa, za a samu karuwar jariran da ake haihuwarsu a kasashen duniya masu tasowa, sabanin kasashen da suka ci gaba, inda haihuwar jariran za ta samu koma-baya, lamarin da zai haddasa gagarumin sauyi a tsakanin al’ummomin ɓangarori biyu.

Tuni dai yawan haihuwa ya ragu a rabin ƙasashen duniya, ta yadda ba za a iya habbaka adadin mutanen ba zuwa mizanin da ake buƙata kamar yadda tawagar daruruwan masu binciken kasa da kasa ta bayyana a ‘Mujallar The Lancet’.

KU KUMA KARANTA: Ko kasan cewa ƙasar Tanzaniya ta fi kowace ƙasa yawan dabbobi a duniya?

Nan da shekara ta 2050, za a samu raguwar kashi daya bisa uku na yawan jama’ar kusan daukacin ƙasashen duniya kamar yadda cibiyar da ta gudanar da bincikenta.

Binciken, ya ayyana Samoa, Somalia, Tonga, Nijar, Chadi da Tajikistan a matsayin ƙasashen da ake sa ran za su samu ƙaruwar al’umma fiye da mizanin da ake buƙata nan da shekara ta 2100.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...