Adadin ƴan jaridar da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kai 132

0
131

Isra’ila ta kashe ƙarin ƴan jarida biyu a wani hari da ta kai musu ta sama a tsakiyar Gaza da aka yi wa ƙawanya, lamarin da ya kai adadin ƴan jaridar da ta kashe zuwa 132, in ji hukumomin Falasɗinu.

A wata sanarwa da ofishin watsa labarai na gwamnatin Falasɗinu da ke Gaza ya fitar, ya ce daga ranar 7 ga watan Oktoba da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare zuwa yanzu, ta kashe ƴan jarida 132, idan aka haɗa da Mohammad Yaghi da Musab Abu Zaid waɗanda jiragen yaƙinta suka kashe ranar Juma’a.

Isra’ila ta kashe ƴan jaridar biyu tare da iyalansu a hari ta sama da ta kai sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat, a cewar hukumomin Falasɗinu.

Dakarun Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa da kuma ta ruwa ne a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba bayan ƙungiyar Hamas ta kai harin ba-zata a Isra’ila sakamakon musgunawar da take yi wa Falasɗinawa da keta haddinsu da mamayar da ta yi wa Masallacin Ƙudus.

KU KUMA KARANTA: Yaran Gaza sun yi zanga-zangar adawa da mamayar Isra’ila ta hana su abinci da ruwa

Hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 29,514, galibinsu mata da ƙananan yara, tare da jikkata fiye da mutum 69,616.

Yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza ya raba fiye da kashi 85 na mazauna yankin da muhallansu inda suke fama da ƙarancin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna, yayin da yaƙin ya lalata kashi 60 na gine-ginen yankin, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

A karon farko tun da aka ƙirƙiri ƙasar Isra’ila a 1948, an gurfanar da ita a gaban kotun ƙasa da ƙasa bisa zargin kisan kiyashi a Gaza.

A watan Janairu, kotun ta bai wa Isra’ila umarni ta daina kisan kiyashi sannan ta bari a kai wa fararen-hular Gaza kayan jinƙai ba tare da shamaki ba.

Leave a Reply