ACReSAL ta ƙaryata faifen bidiyon dake zargin ƙin gudanar da wasu ayyuka a Kano

0
291
ACReSAL ta ƙaryata faifen bidiyon dake zargin ƙin gudanar da wasu ayyuka a Kano

ACReSAL ta ƙaryata faifen bidiyon dake zargin ƙin gudanar da wasu ayyuka a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shirin yaƙi da kwararowar hamada da inganta muhalli a cikin al’umma na jihar Kano (Kano-ACReSAL) ya ƙaryata wani faifan bidiyo da ke yawo, yana zargin gazawa da rashin gaskiya a aiwatar da aikin a faɗin jihar.

A wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta shirin, Maryam Abdulqadir, ta fitar a yau Asabar a Kano, ofishin ACReSAL ya bayyana bidiyon a matsayin ƙoƙari da gangan don yaudarar jama’a.

Sanarwar ta ce an fitar da wannan bayani ne domin amsa tambayoyi da dama daga ’yan jarida da ke neman sahihan bayanai akan zarge-zargen da aka yi a bidiyon.

A cewar Maryam, tun lokacin da aka fara aikin, an samu nasarori da dama a sassa daban-daban na aikin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8.5 don aikin magance zaizayar ƙasa a unguwanni 2 a jihar 

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa bidiyon ya yi zarge-zarge guda uku: cewa a Kano-ACReSAL ba a gina da rijiya mai amfani da hasken rana ba kamar yadda shirin ya tanada, sai kawai aka gina rijiyoyin tuƙa-tuƙa.

A bidiyon, an kuma yi zargin cewa tallafin da aka tsara baiwa al’umma don bunƙasa sana’o’in su, Mai taken ‘Community Revolving Fund’ (CRF) shi ma ba a bayar ba sai kuma cewa ba a taɓa siyan motocin kwashe shara ba kamar yadda shirin ya tanada ba.

Sai dai Maryam ta ƙaryata waɗannan zarge-zarge, inda ta tuna cewa a ranar 6 ga Fabrairu 2025, ƙungiyoyi goma da su ka ci gajiyar shirin sun karɓi takardun cekin kuɗi na dala $25,000 (Naira miliyan 37.5) kowannensu daga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a wani babban taro da aka gudanar a gidan gwamnati.

”Waɗannan ƙungiyoyi sun haɗa da wadanda ke cikin ƙananan hukumomin Gwale, Dala, Madobi da Kabo. Za a ci gaba da rabon tallafin na CRF ga ƙarin ƙungiyoyi a matakai masu zuwa.”

“Haka kuma, dangane da kula da shara, shirin ya tabbatar da sayen manyan motoci 10 da injinan ɗaukar shara guda biyu Kuma an kai su ga domin hukumar kwashe shara ta jiha , warp REMASAB,” in ji ta..

Ta ce kayan aikin, ƙarƙashin sashe na C1, tuni an fara amfani da su a titunan Kano, kuma ana iya tabbatar da hakan ta hanyar ziyartar REMASAB kai tsaye.

Maryam ta ce duk zarge-zargen da aka baiyana a faifen bidiyon ba gaskiya ba ne domin duk aiyukan da ke karkashin shirin na ACReSAL ana nan ana aiwatar da su kuma kowa ya na gani

Leave a Reply