Daga Ibraheem El-Tafseer
Kamfanin fasaha na Apple, ya fitar da sabuwar wayar iPhone 15, ranar 12 ga watan Satumba 2023.
An bayyana wannan samfurin na iPhone 15 a taron “Wanderlust” na kamfanin a Cupertino, California, United States Of America (Amurka), kuma wayar ta fito ne cikin nau’i huɗu: iPhone 15, iPhone 15 Plus, iPhone 15 Pro da iPhone 15 Pro Max, kamar yadda rahoton Forbes ya bayyana.
A nan akwai abubuwa biyar da yakamata a sani game da sabuwar wayar ƙirar iPhone 15.
- Sabon samfurin an yi shi ne da titaniu, ba baƙin ƙarfe ba kamar yadda wasu samfuran wayoyin Apple na Apple suke.
- Samfurin Pro Max ya ƙunshi ƙarfin camera da zuƙowa (zooming) ninki biyu akan iPhone 14. Sannan ta zo tare da sabon gilashi na periscope, na zamani, yana yin zuƙo gani mai nisan 5-6x, fiye da wayoyin baya.
- Samfuran Pro sun zo sauri na ‘A17 bionic’ da ake tsammanin zai sa ta yi sauri matuƙa.
- Ita wannan iPhone 15 ɗin ta zo da gindin caji na USB-C (type-C), irin na wayoyin Android.
- Ana sa ran za a sayar da sabuwar samfurin iPhone 15 ɗin akan farashi mai tsada, saboda murfin titanium da aka yi amfani da shi wajen ƙera ta. A cewar Forbes, ana ta jita-jita na farashin:
iPhone 15, $799, (N800,000)
iPhone 15 Plus: $899, (900,000)
iPhone 15 Pro: $1,099 (1,000,000),
iPhone 15 Pro $1,299 (1,200,000).