Connect with us

Labarai

Abubuwan da gwamnonin arewa suka tattauna a taronsu na Kaduna

Published

on

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun sha alwashin bunƙasa harkar ilimi da fasaha da kula da lafiya da kuma ayyukan walwalar jama’a domin magance matsalar rashin tsaro da yankin ke fama da ita.

Gwamnonin sun yi wannan alƙawari ne a taron da suka yi a jihar Kaduna a ranar Talata, ƙarƙashin inuwar ƙungiyarsu ta Gwamnonin Arewa.

Ga dai wasu muhimman abubuwa da gwamnonin suka tattauna a taron, kamar yadda jawabin bayan taro da mai taimaka wa gwamnan jihar Gombe wanda shi ne shugaban ƙungiyar, kan watsa labarai ya fitar.

KU KUMA KARANTA: Manyan hafsoshin tsaro da gwamnonin arewacin Najeriya sun gana kan satar mutane

  1. Kungiyar ta yaba wa gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, “wanda ya nuna jajircewarsa wajen samun nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka.”
  2. Kungiyar ta nuna matukar tausayawa da goyon baya da ba da hadin kai ga gwamnatoci da al’ummomin Jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Filato da Zamfara kan kalubalen tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a halin yanzu da ya addabe su, a wannan mawuyacin lokaci.
  3. Taron ya yi nuni da cewa yana da matukar muhimmanci a mayar da hankali wajen haɓaka ayyukan ci gaban al’umma da yankin baki ɗaya, tare da nuna damuwa cewa a halin yanzu yankin yana fama da matsaloli kamar na yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.

A don haka ne, gwamnonin suka sha alwashin saka hannun jari mai tsoka a fannin ilimi da bunkasa fasaha da kula da lafiya da kuma ayyukan jin dadin jama’a domin magance matsalar.

  1. Gwamnonin sun karbi rahoton wani kwamitin da zai duba rahoton hukumar New Nigeria Development Company (NNDC), sannan an yanke shawarar cewa mambobin kwamitin su yi nazarin rahoton a taron ƙungiyar gwamnonin na gaba.
  2. Taron ya yi nuni da irin rawar da ake sa ran kamfanin New Nigeria Development Company (NNDC) zai taka wajen farfado da tattalin arzikin jihohin Arewa. A kan haka ne taron ya yanke shawarar saka hannun jari a cikin muhimman ababen more rayuwa wadanda za su iya bude manyan masana’antu da tattalin arzikin Arewa.
  3. Taron ya yi nuni da cewa sauyin yanayi da rashin dorewar ayyukan noma da karuwar jama’a na haifar da gagarumin ƙalubale ga yankin.

Ya kuma ƙuduri aniyar daukar cikakken tsarin da zai inganta kiyaye muhalli da dauwamammen tsarin noma da kula da albarkatun kasa don kare rayuka da rayuwar jama’a da kuma kiyaye al’adun kasa har kan al’ummar da ba ta ma zo ba tukun.

  1. Taron ya saurari bayanai daga shirin bunƙasa ilimin ƴaƴa mata da ƙarfafa musu (AGILE) da kuma wasu bayanan daga tawagar Bankin Duniya. Sannan ya bai wa shirin AGILE da tawagar Bankin Duniya tabbacin samun goyon bayan gwamnonin da kuma buƙatar su da su hanzarta tsarin inganta shirin.
  2. Taron ya kuma karɓi baƙuncin kwamitin zartarwa da kwamitin amintattu na Ƙungiyar Dattijan Arewa Consultative Forum (ACF). Kungiyar gwamnonin ta kuma yanke shawarar bayar da goyon baya da karfafa gwiwar kwamitin amintattun ACF wajen ganin an cimma manufofin shugabannin da suka kafa ta.
  3. Gwamnonin sun kuma karɓi rahoto daga Gamayyar Kungiyoyin Arewa a kan tsaro a Arewacin Najeriya. Ƙungiyar ta yaba wa gamayyar bisa jajircewarta wajen tabbatar da tsaron yankin Arewa tare da yin alkawarin haɗa kai da ita.
  4. Ƙungiyar gwamnonin ta yaba wa shugabanninta kan haɗa hannu da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da shugabannin rundunar soji da gamayyar ƙungiyoyin farar hula na Arewa da sauran masu ruwa da tsaki wajen tsara hanyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa.
  5. Zauren ya yaba wa shugaban kungiyar bisa jajircewarsa wajen ciyar da muradun Arewa gaba. Ƙungiyar ta kuma yabawa mai masaukin baki Gwamnan bisa namijin kokarin da yake yi na karbar bakuncin tarukan dandalin.
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like