Abubuwa 10 da za su iya faruwa idan Tinubu ya zarce a wa’adi na biyu – Hasashen KY Tebo

0
335
Abubuwa 10 da za su iya faruwa idan Tinubu ya zarce a wa’adi na biyu - Hasashen KY Tebo

Abubuwa 10 da za su iya faruwa idan Tinubu ya zarce a wa’adi na biyu – Hasashen KY Tebo

Khaleed Yusuf Tebo Potiskum, ƙwararre ne a fannin tattalin arziƙi wanda yanzu haka yana karatun Degree na uku (PhD) a ƙasar Sin (China) bayan kammala Degree na biyu (Masters) a ƙasar Malaysia duk a fannin tattalin arziƙi.

1. Najeriya ce za ta zama cikin ƙasashe masu fama da baƙin talauci saboda fifita siyasa da ake yi da mayar da hankali kan ci gaban ‘yan siyasa maimakon ci gaban ƙasa da ‘yan ƙasa.

2. Za a rasa masu faɗawa gwamnati gaskiya saboda ba masu kishin ƙasar sai na aljihu, kuma za a tilastawa mutane bin dokokin kama karya da aka samar ta hanyar amfani da ‘yan majalisu marasa kishin ƙasa da sune mafi yawa a majalisun Nijeriya.

3. Ba wanda ya isa ya ƙara yin tasiri da sunan hamayya a Dimokraɗiyya irinta Nijeriya, Tinubu zai kafa ‘yan’uwansa da waɗanda ya ke so su mulki Nijeriya na dindindin kamar yadda ya yi a Legas.

4. Arewa za ta koma kufayi na mabarata saboda jahilcin da ke cikinta, dole ‘yan cikinta su miƙa wuya ta hanyar komawa ƙarƙashin daular Tinubu kamar yadda suka tare yanzu saboda kwaɗayi, masu kuɗin cikinsu da taurin kai za a ƙaƙaba musu takunkumi kan dukiyoyinsu idan ba su bi gwamnati ba.

KU KUMA KARANTA:Tattaunawa: Ƙarfin ƙungiyoyin da ke tattare da ‘Zionism’ da mulkin mallaka a cikin gwagwarmayar Afirka

5. Ta’addanci zai zama ruwan dare, ta yadda talaka zai yi ta ransa ya manta da maganar neman ‘yanci ko wani jin daɗi, malamai da sauran masu faɗa aji a Arewa za a kakkama su idan suka soki gwamnati.

6. Za a raunana doka, za kuma a wulaƙanta masu ruwa da tsaki kan sha’anin doka kamar Lauyoyi da Alƙalai da aka kashe ƙasar da su a baya, kuma za a ci gaba da yin barazana ga rayuwar ‘yan kishin ƙasar ta hanyar kashewa, ɓatar wa ko kullewa.

7. Mata za su shiga masifar da ba su taɓa shiga ba, za su fito neman abinci kan titi irin yadda ba a taɓa yi ba a tarihin Nigeria, kuma cututtukan zamani za su yawaita tsakanin al’umma.

8. ‘Yan mulkin mallaka za su haɗa ƙarfi da ƙarfe su kwashi arziƙin Nijeriya ta hanyar kashe-mu-raba da masu ruwa da tsaki kan harkar mulki tare da juya akalar ci gaban ƙasar kan tsarinsu na Turawa.

9. Matasa za su nemi inda za su gudu, amma ba za su samu kuɗin da za su iya jigilar fita ba, ƙarshe kowa zai rasa aikinyi, za a rufe kasuwanni ta hanyar rasa jari da hauhawar farashi na tashin hankali, daga ƙarshe rayuwa za ta jefa mutane tsanani saboda karyewar darajar Naira gabaɗaya.

10. Daga ƙarshe za a iya fito na fito da gwamnati ta hanyar juyin juya hali, kuma za a iya tunzura ƙasar dan a yi yaƙi, daga ƙarshe idan ba a hankalta ba Nijeriya za ta shiga masifar yaƙi ne saboda ba lalle a samu sasanci tsakanin masu ƙwatar ‘yancin ƙasar ba da suke mabambanta manufa.

Leave a Reply