Abin da ya sa sabuwar wayar iPhone 15 take ɗaukar zafi

0
234

Kamfanin Apple ya ɗora alhakin zafin da sabuwar wayarsa ta iPhone 15 ke yi a kan wata ƙwaya mai cutar wa da ke cikin injin sarrafa wayar da kuma ayyukan sabunta manhajoji kamar Instagram.

Tun lokacin da kamfanin ya fara sayar da sabuwar wayar da ya fitar a watan Satumba, wasu masu amfani da iPhone 15 suka fara ƙorafin cewa wayoyin nasu na ɗaukar matuƙar zafi.

Apple ya ce akwai wata ƙwaya mai cutar wa a duk lokacin da aka sabunta injin sarrafa wayar wato iOS 17.

Ya kuma yi iƙirarin cewa sauye-sauyen da ake samu a kan manhajojin wasu kamfanonin ne ke “janyo su cika injin sarrafa wayar”.

Masu amfani da iPhone su kwan da sanin cewa wayoyinsu kan ɗauki ɗan zafi a farkon lokacin da suka fara amfani da su, ko kuma idan wayoyin na aika wasu bayanai zuwa babban rumbun adana bayanai saboda yawan lantarkin da suke ja da kuma aikin da wayar take yi fiye da ƙima, sai dai lamarin ya fi muni ga wayoyin iPhone 15.

KU KUMA KARANTA: WhatsApp zai daina aiki a wasu wayoyin Android da iPhone

Masu amfani da wayar sun hau shafukan sada zumunta don yin ƙorafi a kan yadda sabbin wayoyin suke ɗaukar zafi.

Apple ya ce mai yiwuwa ne wayar takan ɗauki zafi cikin kwanaki ƙalilan na farko “bayan kunna wayar ko kuma sake adana bayanan da take tattarawa saboda ƙaruwar aikace-aikace a bayan fage.”

Kamfanin ya ce: “Mun fahimci waɗansu yanayi ƙalilan da ke iya sanya wa wayoyin iPhone su ɗauki zafi fiye da yadda ake tsammani.”

Leave a Reply