Abin da ya sa muka kai shugaban ƙaramar hukumar Potiskum ƙara majalisar jiha – YSUF

0
280
Abin da ya sa muka kai shugaban ƙaramar hukumar Potiskum ƙara majalisar jiha - YSUF

Abin da ya sa muka kai shugaban ƙaramar hukumar Potiskum ƙara majalisar jiha – YSUF

Daga Ibraheem El-Tafseer

A makon da ya gabata ne, Neptune Prime Hausa ta yi hira da shugaban ƙungiyar haɗin kan Yobe ta Kudu (Yobe South Unity Forum), Malam Hassan B. Joda. A hirar ta su ya bayyana manufa da hadafin ƙirƙirar wannan ƙungiya da irin ayyukan da ta saka a gaba.

Sannan ya bayyana irin nasarori da kuma ƙalubale da wannan ƙungiya ta ke fuskanta. Editanmu na sashen Hausa, Ibraheem El-Tafseer ne ya yi hirar da shi, ga yadda hirar ta su ta kasance;

NEPTUN PRIME HAUSA: Ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

HASSAN BOMAI JODA: Sunana Hassan Bomoi Joda, ni ne shugaban ƙungiyar Haɗin Kan Yobe Ta Kudu (Yobe South Unity Forum).

NEPTUN PRIME HAUSA: Menene manufa da hadafin ƙirƙirar wannan ƙungiya ta ‘Yobe South Unity Forum’?

HASSAN BOMAI JODA: Mun ƙirƙiri wannan ƙungiya ce a watan Oktoba na shekarar 2023, a wannan watan ta cika shekara ɗaya cif-cif da ƙirƙirar ta. Manufa da hadafin da ya sa muka ƙirƙire ta shi ne, ganin yadda yankinmu na Yobe ta Kudu (Zone B) take ci baya ta ɓangarori da yawa, sakamakon rarrabuwar kai a tsakaninmu.

To wannan shi ne ya sa muka ga ya dace mu ƙirƙiri ƙungiya domin a kawo ƙarshen wannan rarrabuwar kan da yake haifar mana da ci baya a wannan yanki na mu.
Wannan rarrabuwar kan ya kawo ci baya a kusan komai a yankin, tun daga harkar ilimi, lafiya, musamman ma ta ɓangaren harkar siyasa. Duk wani ci gaba a siyasance to mu a wannan yankin an bar mu a baya.

NEPTUN PRIME HAUSA: Wace nasara wannan ƙungiya ta samu daga kafa ta zuwa yanzu?

HASSAN BOMAI JODA: Mun yi ƙoƙari mun samar da haɗin kai tsakanin matasa a wannan yankin. Yanzu irin zage-zage da ake a kafafen yaɗa labarai na zamani, yanzu sun ragu matuƙa. Daga cikin nasarar da muke lissafa wa wannan ƙungiya ta samu, akwai daƙile ƙabilanci a wannan yanki na Yobe ta Kudu.

NEPTUNE PRIME HAUSA: Menene alaƙar wannan ƙungiya da siyasa?

HASSAN BOMAI JODA: Eh lallai wannan ƙungiya tana harkar siyasa, amma siyasar mu ba ta jam’iya ba ce. Domin kuwa duk abin da da akwai shugabanci a ciki, to akwai siyasa. Abin da ya sa na ce siyasarmu ba ta jam’iya ba ce, shi ne mambobin wannan ƙungiyar sun haɗa mutane daban-daban daga jam’iyyu daban-daban.

KU KUMA KARANTA: Wasu matasa a Bauchi sun ƙone ɓarayin adaidaita sahu har lahira

NEPTUNE PRIME HAUSA: Menene ya ja hankalinku kuka kai shugaban ƙaramar hukumar Potiskum ƙara majalisar jiha?

HASSAN BOMAI JODA: Da gaske ne mun rubuta takarda ta ƙorafi a majalisar jiha, akan shugaban ƙaramar hukumar Potiskum, Alhaji Salisu Mukhtari, kan rashin rantsar da Sakataren ƙaramar hukuma da kuma Kansiloli.

Wanda hakan saɓa wa doka da oda na gudanarwar ƙaramar hukuma. Dokar gudanarwa na ƙananan hukumomi, an ƙirƙire ta a shekarar 1987. To ya karya wannan doka, domin kuwa ya tafiyar da mulkinsa na kwanaki 100 ba tare da sauran waɗanda doka ta haɗa masa ya tafiyar da mulkin tare da su ba.

Daga shi sai mataimakinsa suke tafiyar da mulkin. Sannan dokar ƙananan hukumomi ta jihar Yobe, ita ma kwanaki 30 ta ba shi ya rantsar da Sakatare da Kansiloli. Wannan dokar ma ya karya ta. Sannan a waɗannan kwanaki 100 da ya yi, bai zauna a ofis na kwana 10 ba, kullum ba ya nan.

Mu babban abin da ya ja hankalinmu ma shi ne, wannan jinyace-jinyace da ake ta fama da shi, asibiti kullum a cike da marasa lafiya, amma babu wani agaji daga ƙaramar hukuma. Sai muka fara binciken me yake faruwa? Soboda mun ga ƙungiyoyi na wasu matasa suna haɗa kuɗi suna sayen maganin kashe sauro, suna bi unguwa-unguwa suna feshi.

Amma babu wani agaji daga ƙaramar hukuma. To wannan shi ne ya sa na ƙira mambobin wannan ƙungiya, muka ce ya kamata a ja hankalin gwamnati. Gwamnatin farko kuma ita ce ƙaramar hukuma, domin ita ce take kusa da talaka. Daman kuma daga cikin manufofin wannan ƙungiya akwai jan hankalin gwamnati, idan ba ta yin daidai.

To wannan bincike da muka yi, na rashin agaji daga ƙaramar hukuma, a nan muka fahimci bai zauna a ofis na kwana 10 ba, a kwanaki sama da 100 da ya tafiyar da mulkinsa. Shi ba ya nan, sannan bai bayar da dama ga mataimakinsa ya yi ayyuka ba. Sannan babu sakatare, babu kansiloli.

NEPTUNE PRIME HAUSA: Bayan shigar da ƙorafinku, wane mataki majalisa ta ɗauka a kansa?

HASSAN BOMAI JODA: Gaskiya na jinjinawa majalisar jihar Yobe. Sun sake ƙiranmu mu zo maimaita ƙorafin namu, muka je muka tabbatar musu da ƙorafin namu. Sannan shi ma shugaban ƙaramar hukuma ɗin, Salisu Mukhtari daga baya suka ƙira shi, ko zai iya kare kansa.

Za mu iya cewa, ƙorafinmu da muka kai, kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Domin kuwa a cikin ƙorafin namu, mun ce su tilasta shi ya rantsar da Sakataren ƙaramar hukuma da Kansiloli. Kuma a ranar suka ba shi umarnin da ya je ya rantsar da su. Alhamdulillah! Zuwa yanzu an rantsar da su.

NEPTUNE PRIME HAUSA: Wane ƙalubale kuke fuskanta a gudanar da wannan kungiya?

HASSAN BOMAI JODA: Lallai muna fuskantar ƙalubale sosai, musamman a wajen ‘yan siyasa da su da ‘yan korensu. Kasan daga cikin dabarun ‘yan siyasa akwai rarraba kan al’umma. Sai sun raba kan mutane suke cin burinsu na siyasa.

Duk ranar da ka zo da wani abu na haɗin kan mutane, to su a wajensu, ka zo da takobin yaƙi da sune. Don haka su ma za su zare takobin yaƙi daku.

To muna fama da su sosai. Su saka yaransu, su ci mana mutunci, su zage mu, su ɓata mana suna. Wasu su yi ta mana ƙage da sharri, cewa wai wasu ne suke ɗaukar dawainiyar mu.

Wasu suna cewa wannan ƙungiya ba za ta ɗore ba, don an yi irin wannan ƙungiya da yawa ba su ɗore ba.

To mu kuma ga shi yanzu mun shekara cif, muna gudanar da wannan ƙungiya. Kuma a manufa da hadafinta babu abin da za mu daina. Barazana, ƙage da sharri ba zai saka mu sare ba.

Leave a Reply