Abin da ya sa muka dakatar da Alƙalan kotunan Majistiri 3 - Hukumar kula da shari'a ta jihar Kano

Abin da ya sa muka dakatar da Alƙalan kotunan Majistiri 3 – Hukumar kula da shari’a ta jihar Kano

Abin da ya sa muka dakatar da Alƙalan kotunan Majistiri 3 – Hukumar kula da shari’a ta jihar Kano

Daga Idris Umar, Zariya

Hukumar kula da harkokin Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta dakatar da Alƙalan Kotun Majistare uku saboda samun su da laifi a yayin gudanar da ayyukansu.

Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya sanar cewa an dakatar da alƙalai uku daga ayyukan shari’a, yayin da aka bayar da takardar gargaɗi ga magatakardar kotu guda ɗaya.

Alƙalan da aka dakatar sun haɗa da Talatu Makama ta kotun Majistare Mai lamba 29, da Babbar Majistire Rabi Abduƙadir ta Kotun Majistire mai lamba 48 da Alƙalin kotun Majistire mai lamba 60, Tijjani Saleh Minjibir.

Na huɗunsu shi ne Magatakarda Abdu Nasir da ke sashin ɗaukaka ƙara da ke Babbar Kotun Jihar Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin karɓar korafe-korafen jama’a na ɓangaren shari’ar ya samu Alƙali Talatu Makama da laifin rashin ɗa’a inda ta bayar da umarni ga Bankin GT ya tura kuɗi zuwa asusun mai shigar da ƙara bayan ta san cewa asusun a rufe yake, inda daga ƙarshe aka sanya kuɗin cikin asusunta.

Haka kuma Hukumar ta same ta da laifin nuna rashin ƙwarewa inda taje karɓar shari’a tare da bayar da oda ga ’yan sanda tun kafin shari’ar ta zo gabanta.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ƙwace dala milyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830 da sauran kadarori daga hannun Emefiele

“Saboda haka an sauke Babbar Alƙali Talatu Makama daga kujerarta an kuma dakatar da ita daga dukkan ayyukan shari’a nan take.

“Sai dai wannan bai shafi kasancewarta ma’aikaciyar gwamnati ba,” in ji sanarwar.

Takarda ta ci gaba da cewa, bayan binciken Hukumar ta JSC kan dambarwar shari’ar da ke tsakanin ƙwamishinan ’yansanda da wani Abubakar Salisu da ke gaban Alƙalin Kotun Majistare Mai lamba 48 Rabi Abduƙadir, an same ta da laifin yin sakaci a shari’a.

“Don haka hukumar ta dakatar da ita daga aikin shari’a na tsawon shekara guda.

“Sannan an umurce ta da ta daina duk wani aiki a Kotun Majistare mai lamba 48.”

Hukumar ta kuma dakatar da Alƙalin Kotun Majistire mai lamba 60 Tijjani Saleh Minjibir na tsawon shekara 1 bisa samun sa da laifin rashin ɗa’a.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *