No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana riko da tsarin nan na “safe school initiative” a matsayin sirrin da ya sa ba cika samun labarin satar ‘yan makaranta ba a jihar.

Tsarin na “safe school initiative” dai wani shiri ne da ya wajabta gina katanga da ɗaukar ma’aikata masu ɗauke da makamai domin kare lafiya da dukiya a makarantu.

Zulum ya bayyana ne Fadar Gwamnatin Najeriya jim kaɗan bayan fitowarsa daga wani taro na shuwagabanni a ƙasar nan.

Zulum ya ce “Mun kai aƙalla shekara bakwai zuwa takwas da ƙaddamar da tsarin ‘Safe School Initiative ’ a Jihar Borno.

KU KUMA KARANTA: Rikici ya raba yara miliyan 1.8 da muhallansu a yankin Sahel – Save The Children

“Kusan duk makarantunmu na da katanga, mun gayyaci sojoji da ’yan sanda aikin tsare ɗalibai da makarantunmu.”

Zulum ya ƙara da cewa “Mun ɗauki ’yan banga da ’yan sa-kai suna taimaka wa jami’an tsaron kasar nan yadda ya kamata wurin tabbatar da tsaro a makarantun Jihar Borno.”

Gwamna Zulum ya jinjina wa jami’an tsaron bisa ƙoƙarin da ya ce suna yi wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Borno da sauran sassan ƙasar nan.

Jihar Borno dai ɗaya ce daga cikin jihohin da suka sha fama da bala’in ta’addancin kungiyar Boko Haram da ISIS masu tada ƙayar baya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...