Abin da ya sa aka dakatar da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars

0
6
Abin da ya sa aka dakatar da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars

Abin da ya sa aka dakatar da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar gudanarwar Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƙungiyar Usman Abdallah na tsawon makwanni 3.

Dakatarwar ta biyo bayan rashin tabuka abin a zo a gani a baya bayan nan, da kuma harzika magoya bayan kungiyar, bayan tashi daga wasan da Kano Pillars din ta buga chanjaras da Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha dake Jihar Kano.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar Liverpool ta samu tazarar maki 8 akan teburin gasar Firimiya

Sanarwar da Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar Alhaji Ali Na-yara Maisamba ya sanyawa hannu ta ce, mataimakin mai horas da kungiyar, Ahmad Garba Yaro-Yaro ne zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar kafin kwamitin bincike da hukumar gudanarwar Pillars din ta kafa ya bayar da rahotansa.

Leave a Reply