Abin da ya sa aka cire ni daga sarautar Mujaddadin Bauchi — Sanata Shehu Buba
Na samu labari mai cike da ban mamaki game da wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Augusta inda ake sanar dani cewa Majalisar masarautar Bauchi ta cire ni daga muƙamin sarautar mujaddadin Bauchi sakamakon zargin cewa na ci mutunci ko zagin Gwamnan jihar Bauchi a wani gangamin yaƙin neman zaɓe.
Ina amfani da wannan dama in sanar da cewa tun sanda na shiga siyasa ba na bin wani tsari fa ce suka mai ma’ana, ba tare da cin mutunci ko zagi ba, kuma tsarin da nake bi tsari ne na nufin samar da ingantacciyar al’umma.
Lokacin da na saurari kalaman Gwamna Bala Muhammad akan Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu sai na ga hakan ya kasance wajibi gare ni da na kare shugaban ƙasar daga yunƙurin da ake yi na ɓata wa da lalata ƙimar sa da saka ƙiyayyar sa a zukatan al’umma, wanda haka na yi a yaƙin neman zaɓen da APC ta yi da na halatta kwanan nan .
Amma Kuma maganganun Gwamna Bala Muhammad akan Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu wanda kafafen yaɗa labaran ƙasar nan da dama suka rawaito sun haɗa da fito na fito, da zargi marar tushe da kuma ƙage, da amfani da kalamai da ka iya kawo barazana ta tsaro a ƙasa a maimakon dalilai na hankali.
Kuma ina so in jaddada cewa zarge zargen da Gwamna Bala Muhammad ya yi wa Shugaba Tinubu, kalamai ne na siyasa, ba su da tushe, haka kuma ba su da wata cikakkiyar hujja da dalilai.
Sannan a kalaman da na yi na musanta zargin da Gwamna Bala ya yiwa Gwamnatin Tinubu na rashin kula da aiki da kare haƙƙunan al’ummar ƙasa amma na zargi Gwamna Bala da aikata hakan.
Sannan a jawabin da na yi nace Gwamna Bala Muhammad ya karɓi Naira Biliyan 144 daga asusun Gwamnatin Tarayya a Shekarar 2023 da kuma fiye da Naira Biliyan 47 daga watan Janairu zuwa yau wanda ake sa ran a jumlace za su kai Naira Biliyan 195 zuwa ƙarshen wannan shekarar, inda na nemi bahasi akan cewa me Gwamnatin Bala Muhammad ta yi da waɗannan kuɗaɗen.
Saboda haka na ƙara da cewa zargin da Gwamna Bala ya yiwa Shugaba Tinubu ba su da tushe ballantana makama kuma kalamai ne na siyasa.
Sannan a jawabina na tuhumi Gwamna Bala Muhammad da ya faɗi abin da ya yi da maƙudan kuɗaɗe da ke asusun Jihar ta Bauchi sakamakon yadda al’umma ke kukan yunwa duk da cewa Gwamnatin ta karɓi biliyoyin Naira daga asusun Gwmantin Tarayya.
KU KUMA KARANTA:Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi
Sannan nace Shugaba Bola Ahmad Tinubu na yin iya ƙoƙarinsa na samar da tsaro a faɗin tarayyar Najeriya, da daidaita tattalin arziƙi da kuma ganin an samu zaman lafiya tsakanin ‘yan ƙasa ba tare da rabuwar kai ba Wanda Shi Gwmana Bala ba haka yake ba.
Kalamai na na yi su ne da kyayyakwar niyya da Kuma Kare shugabanci na sama ba na matakin Jiha ba.sannan ina mamaki da nadamar yadda Majalisar masarautar Bauchi ta gaggauta Yanke hukunci akan kalamai na ba tare da taji ta bakina ba,saboda haka matsayar da Majalisar masarautar ta Bauchi ta yanke akai na na karba da kyakkyawar niyya ,sannan ina da saka rai cewa Allah madaukakin sarki zai aiko da wani maceci da zai zo ya ceci jihar Bauchi daga halin da take ciki.
Sannan Ina shawartar Majalisar masarautar Bauchi da ta guji amfani da wasu ka iya yi da ita domin cimma manufofin su na san Rai da Kare muradun wasu .Sannan ina Addua Allah ya ja zamanin mai martaba Sarkin Bauchi da lafiya domin tafiyar da wannan masarauta.
A wannan jawabi nawa na hada da Kwafin zargin da Gwamna ya yiwa Shugaba Tinubu a shirye shirye da akayi da shi kai tsaye tare da Kuma martani da na mayar.
Ina Godiya matuka Kuma Ina Mika jinjina da Gaisuwa
Sa hannun
Sanata Shehu Buba Umar
Shugaban Kwamitun Majalisar Dattijai na tsaro da tattara bayanai.