Abdulaziz Abdulaziz ya zama mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai

0
329

Daga Ibraheem El-Tafseer

An naɗa Abdulaziz Abdulaziz, fitaccen ɗan jarida daga Arewacin Nijeriya a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu kan harkokin yaɗa labarai.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin jerin sunayen mataimaka na musamman da masu ba da shawara da shugaban ya naɗa a kwanan nan.

Wannan matsayi mai daraja da Abdulaziz Abdulaziz ya samu ya nuna hazaƙa da himmarsa a matsayinsa na ɗan jarida, inda ya bar baya da kyawawan nasarori a tsawon rayuwarsa aikinsa.

Har wala yau naɗin Abdulaziz wata shaida ce da ke nuna jajircewarsa a fagen aikin jarida da kuma nagartaccen ayyukansa.

Leave a Reply