Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ne ya yi wannan kiran a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce yin rufa-rufa kan lamarin da kuma dakatar da wanda ya kwarmata zancen ba mafita ba ce.
Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023, Atiku, ya ce akwai buƙatar a gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike kan zargin cushe a kasafin kuɗin Najeriya na 2024.
A ‘yan kwanakin nan ne Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar mazaɓar tsakiyar yankin jihar Bauchi a Majalisar Dattawa, ya yi zargin cewa an yi cushen sama da Naira tiriliyan uku a kasafin kuɗin 2024.
Majalisar ta musanta zargin ta kuma dakatar da shi tsawon watanni uku daga halartar zaman majalisar bayan da akasarin mambobinta suka amince da hakan.
Sai dai Atiku ya ce ‘yan Najeriya na da haƙƙin su ga an gudanar da bincike kan zargin da Ningi ya yi.
“Musanta cewa babu wani abu kamar haka, da dakatar da Sanatan da ya kwarmata zancen, ba za su hana zargin cewa akwai matsalar cin hanci da rashawa da kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba da gwamnatin tarayya ke yi.
“Ba zai yi wu a yi rufa-rufa kan zargin yin cushe a kasafin kuɗi da yawansa ya kai Naira tiriliyan uku ba.” In ji Atiku.
KU KUMA KARANTA:Manyan Sanatoci sun kai wa Tinubu ziyara bayan dakatar da Sanata Ningi
Atiku ya ƙara da cewa, “duba da irin wahalar da ake fuskanta a Najeriya, cushe a kasafin kuɗin ƙasa na nufin karin yunwa, talauci, rashin tsaro da rashin wutar lantarki da matsalar canja kudaden ƙasashen waje da kuma tsadar rayuwa.”
“Babu yadda za a ce ‘yan Najeriya za su naɗe hannayensu suna kallo a yi watsi da wannan zargi da ke kara ta’azzara matsalar tattalin arziƙinmu.” In ji Atiku.
Najeriya ta ware Naira tiriliyan 28.7 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2024.