A wata 6, hatsarin mota ya kashe sama da mutane 2,800 – FRSC

0
159
A wata 6, hatsarin mota ya kashe sama da mutane 2,800 – FRSC

A wata 6, hatsarin mota ya kashe sama da mutane 2,800 – FRSC

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Kiyaye Hadurran Hanya ta Ƙasa, FRSC, ta ce an samu haɗurran mota 5,281 a faɗin Najeriya daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025, inda mutane 2,838 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 17,818 suka tsira da ransu.

Kwamandan hukumar, Shehu Mohammed, ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa adadin haɗurran da kuma yawan mace-macen da suka biyo baya sun ƙaru idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata – da kashi 3.9 cikin ɗari .

Ya ce gabaɗaya, mutane 39,793 ne haɗurran suka shafa a cikin wannan lokaci, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 8.9 cikin ɗari idan aka kwatanta da makamancin lokaci a shekarar 2024.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Daura zuwa Katsina

Hukumar ta kuma ce ta kama mutane 290,887 bisa aikata laifukan da suka shafi dokokin hanya 319,798, adadi mafi yawa idan aka kwatanta da 250,720 da aka kama a shekarar da ta gabata bisa laifuka 271,895.

Leave a Reply