Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP, Olukayode Egbetokun ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai wa wani jami’in ‘yan sanda, Insp. Omeje Matthew a Abuja.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce I-G ya ba da wannan umarni ne a lokacin da ya ziyarci jami’in da ke jinya a asibitin ƙasa da ke Abuja.
Mista Egbetokun ya ce sun kai ziyarar ne domin duba halin da jami’in da wasu ‘yan bindiga suka kai masa a gidansa da ke unguwar Kabusa a birnin tarayya Abuja.
Ya umarci kwamishinan ‘yan sanda (CP) mai kula da babban birnin tarayya Abuja da ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe sojojin Nijar a yankin Tillabery
A cewarsa, binciken shi ne don tabbatar da cewa an gaggauta cafke waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya.
IG ya kuma buƙaci sauran kwamishinonin ‘yan sanda da kwamandojin Dabarun da su tabbatar da rufe duk wani bincike da ake yi kan hare-haren da ake kai wa jami’an ‘yan sanda da a yankunansu.
“Harin da aka kai wa jami’in ‘yan sanda da ke bakin aiki ko kuma ba ya aiki, hari ne ga ɗaukacin jami’an tsaro da zaman lafiya da tsaron al’ummarmu,” in ji shi.
Ya nuna rashin gamsuwa da hare-haren da ake kai wa jami’an ‘yan sanda, ya kuma yi gargadɗin cewa ba za a amince da irin waɗannan hare-haren ba.
Shugaban ‘yan sandan ya yi addu’ar Allah ya ba sufeton ‘yan sandan da sauran waɗanda ke cikin wannan hali lafiya.
Ya kuma yi alƙawarin ɗaukar nauyin rundunar ‘yan sandan Nijeriya na tallafa wa da kuma taimaka wa iyalan jami’an da abin ya shafa.
Mista Egbetokun ya buƙaci jama’a da su bai wa ‘yan sanda haɗin kai wajen bayar da bayanan da ka iya kawo ƙarshen hare-haren da ake kaiwa jami’an ‘yan sanda.