A gaggauta sakin Jamila Ibrahim da jaririnta – Amnesty International

0
353
A gaggauta sakin Jamila Ibrahim da jaririnta - Amnesty International
Jamila Ibrahim ɗauke da jaririnta da suke tsare tare

A gaggauta sakin Jamila Ibrahim da jaririnta – Amnesty International

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira da a gaggauta sakin Jamila Ibrahim ba tare da wani sharaɗi ba, wacce ‘yan sandan Najeriya suka kama a kasuwar Wuse da ke Abuja a ranar 28 ga watan Maris a yayin da take ɗauke da jaririnta mai watanni ɗaya a lokacin da suke gudanar da muzaharar ranar Ƙudus cikin lumana, wanda aka gudanar a ƙarshen azumin watan Ramadan.

Jamila da jaririnta har yanzu suna tsare a gidan yari na Suleja ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba, ko kuma ga dangi ko lauya, ba tare da bin doka da oda ba.

Ci gaba da tsare Jamila da jaririnta a gidan yari ba bisa ƙa’ida ba, wani mataki ne da hukumomin Najeriya ke yi akai-akai, ba bisa ƙa’ida ba, hakan yana nuna rashin tausayi da kuma ƙoƙarin murƙushe Harkar Musulunci a Najeriya da magoya bayanta.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansandan Najeriya sun kashe mutane 24 a zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta – Amnesty

Tun daga watan Disambar 2015, an kashe ɗaruruwan mambobin Harkar Musulunci, almajiran Sheikh Zakzaky ciki har da jarirai. Jami’an tsaron Najeriya a kullum suna tunkarar jerin gwanon (Muzahara) lumana da mabiya Harkar Musulunci ɗin suke yi, da nufin kashe mutane, ba wai don tabbatar da doka da oda ba.

Wannan tsarewa ba bisa ƙa’ida ba da kuma murƙushe ‘yan ƙungiyar ta Harkar Musulunci bai dace ba kuma ba za a amince da shi ba. Suna da haƙƙinsu na gudanar da zanga-zangar addini ta lumana kuma babu wata shaida da suka haifar da barazana ga rayuwar kowa a tsawon shekarun da suka ɗauka suna gudanar wa.

Rashin ci gaba da gudanar da bincike game da wannan babban take haƙƙin ɗan’adam yana ƙara haifar da ƙyama ga tsarkakar rayuwar ɗan’adam da bin doka da oda a Najeriya.

Leave a Reply