A gaggauta biyan Malam Bature Jibrin haƙƙoƙinsa – Gwamna Uba Sani

0
16
A gaggauta biyan Malam Bature Jibrin haƙƙoƙinsa - Gwamna Uba Sani

A gaggauta biyan Malam Bature Jibrin haƙƙoƙinsa – Gwamna Uba Sani

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamna Uba Sani na Kaduna, ya nemi a kawo masa Malam Mohammed Bature Jibrin wanda hotunansa suka karade shafukan sada zumunta cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kore shi aiki a shekara ta 2020 kuma ba a biya shi hakkokinsa na aiki ba wanda hakan ya yi sanadiyar samun tabin hankali.

Yanzu haka dai Gwamna Uba Sani ya ba shi hakuri, ya kuma yi masa alheri, sannan kuma ya bayar da umurnin a gaggauta biyan shi hakkokinsa kafin nan da makon gobe. Sannan Gwamnan ya kira taro da Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna don binciko duk masu matsaloli irin wannan musamman wadanda aka kore su aiki ko suka yi ritaya amma ba a biya su ba a biya su hakkokinsu ba

Hakan ya biyo bayan kira da aka rinƙayi ne ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna akan halin da shi malam Muhammad Bature Jibiril ya faɗa sakamako korar da tsohuwar gwamnati tayi masa.

Shi malam Mohammed Bature Jibrin. Quantity Surveyor ne yayi karatu a ABU Zaria yafito da first class yayi NYSC din shi a kaduna. Saboda jajircewan sa aka bashi Aiki a Kaduna State, Daga 1987 zuwa 2020, kafin ya bar Aiki sai da ya kai matsayin Director a Ministry of Works, Housing and Transport.

KU KUMA KARANTA:Gwamna Uba Sani ya ziyarci ɗaliban makarantar Kuriga da aka sako (Hotuna)

Yana kan aikin sa sai wancen Gwamnatin ta sauke shi a cikin shirinta na rage ma’aikata ba tare da biyan sa hakin saba ko kwabo ba’a bashi ba, Ba fansho ba Garaduti shekara biyar kenan.
Tunda yabar aiki, shine Mai sharan masallaci kuma ladanin Massalacin dake SkyPet layin Mai Anguwa Abdullahi road Rigachikun. Wani lokacin ma Yana limanci.

Ya samu tabin hankali saboda rashin biyansa hakkin sa da Gwamnatin da ta wuce batayi ba har yakai da an dakatar dashi daga limancin da yakan taimaka wasu lukutan.

A yanzu Yana karban magani a Asibitin masu lalurar kwakwalwa dake Barnawa.

Cikin ikon Allah yanzu rahoto da ke yawo a shafukan sada zumunta shine gwamnan jihar Kaduna ya kira malam Jibiril har ya dauki matakin gaggawa akan lamarin

Leave a Reply