A daina yafe wa waɗanda aka samu da cin hanci da rashawa – Fagbemi

0
79
A daina yafe wa waɗanda aka samu da cin hanci da rashawa – Fagbemi

A daina yafe wa waɗanda aka samu da cin hanci da rashawa – Fagbemi

Ministan shari’a kuma Babban Lauyan Ƙasa, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya buƙaci a daina yafe wa duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.

Minista Lateef ya bayyana haka ne ranar Litinin a Abuja, yayin wani taron tattaunawa da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta shirya wa kwamishinonin shari’a na jihohi.

Wata sanarwa da mai taimaka wa Ministan kan hulɗa da jama’a da watsa labarai Kamarudeen Ogundele ya fitar ranar Litinin, ta ce ministan ya ƙudiri aniyar bujiro da wannan batu a gyaran kundin tsarin mulki da za a yi nan gaba.

“Idan aka zo gyaran kuɗin tsarin mulki nan gaba, zan ba da shawara a cire yin afuwa ga duk wanda aka samu da cin hanci da rashawa daga cikin ‘waɗanda gwamnati za ta iya yi wa afuwa’ don hakan ya zama izina ga wasu,” a cewar ministan.

KU KUMA KARANTA: Muna zuba jari a ɓangaren fasaha domin yaƙi da cin hanci – Tinubu

Ya ƙara da cewa “babu dalilin da zai sa a ringa nuna cewa cin hanci da rashawa da aikita laifuka abubuwa ne masu kyau.”

Minista Lateef ya kuma shawarci hukumomin tsaro su kauce wa binciken je-ka-na-yi-ka, yana mai kira a gare su su kammala tattara hujjojinsu kafin su gayyaci wani don amsa tambayoyi.

Fagbemi ya shawarci kwamishinonin shari’a su guji nuna son kai, da bita-da-ƙullin siyasa da yin fushi da fushin wani a yaƙi da cin hanci da rashawa, don kawai suna so su burge gwamnoninsu.

A baya, wasu gwamnatocin tarayya a Najeriya sun yafe wa wasu tsofaffin gwamnoni da aka samu da laifin cin hanci da rashawa da sace dukiyoyin al’umma, har ma aka tsare wasu a gidajen yari.

Leave a Reply