Admiral Dewu ya gina Asibiti a garin Samarun Zariya

0
6
Admiral Dewu ya gina Asibiti a garin Samarun Zariya

Admiral Dewu ya gina Asibiti a garin Samarun Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

A cikin wannan makon ne aka gudanar da bikin bude Asibitin da Admiral Dewu ya kawo yankinsa na Samaru don taimakawa jamar’sa ƙarƙashin hukumar rundunar sojan Ruwa ta ƙasa wato (Nigerian Navy).

Wakilinmu na cikin wakilan kafafen yaɗa labarai da suka halarci taron, ga tsaraba ga masu karatunmu.

Shidan wannan asibiti an assasashi ne shekaru masu yawa basa jagorancin wasu dattawan cikin garin na Samaru dake karamar hukumar Sabon Garin ta jihar Kaduna.

Ganin yadda garin ke ƙara binƙasa yasa ƙaramar hukumar Sabon Garin ta karbi ragamar tafida harkokinsa asibitin karkashin gwamnatin jihar Kaduna.

A cikin wannan tafiyarne Admiral Dewo ya kawo nashi tallafin na sake sabon tsari tare da ƙara faɗin Asibitin da wasu muhimman aiki banda ƙara faɗaɗashi wanda an kashe kuɗi masu yawan gaske.

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari ne ya ja ragamar aikin faɗaɗashi ginin wato injiniya Muhammad Usman Ibrahim tun daga farko har zuwa ƙarshensa.

A jawabin tsohon shugaban ƙaramar hukumar ta Sabon Garin yayin ƙaddamar da wannan asibitin yace, a gaskiya sunyi farin ciki da samun irin su Admiral Dewu a garin Samaru kuma ya tabbatar da cewa duk da hukumar NIGERIA NEVY ce ta gina amma Admiral Dewu ya ɗauki kaso mai yawa cikin aiki don haka yayi jinjina da hakan.

Shima babban bako a wajan Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla ya nuna jin daɗinsa a yayin da yake ƙaddamar da asibitin a lokacin har yace wannan somin taɓi ne da ikon Allah irin wannan aikin alheri na ɗamfare a zuciyar cibiyar tasu sojan ruwa.

Karshe yayi yabo ga shi Dewu bisa wannan kokari na ganin aikin ya tabbata yace, gaskiya ya fitar da hukumarsa kunya kuma yayi roƙo ga jama’ar garin Samaru da kewaye da suyi amfani da wannan asibitin ta hanyar da ya dace.

Shima mai gayya mai aikin Admiral Ibrahim A Dewu a nashi jawabin cewa yayi ya godewa Allah da yaga wannan rana kuma yayi farin ciki da yabo ga dukkan wanda suka bayar da gudummawa har wannan asibitin ya kammala tun daga ƙasa har sama.

Dewu, yayi farin ciki da zuwan babban bako kuma mai gidansa kuma yayi riƙon ga dukkan ɗaukacin jama’ar garin Samaru da kewaye da suyi amfani da wannan asibiti ta hanyar daya dace.

KU KUMA KARANTA:An naɗa sabon darakta a kwalejin kiwon lafiya ta Al-Haroon Zariya

Daga cikin manyan baki da suka hallaci wannan taro akwai wakilin gwamnan jihar Kaduna malam Uba Sani wanda sakataren hukuman lafiya ta jiha Dakta Bello Yusuf Jamoh yazo a madadinsa kuma ya baiyana jinjina da gwamna yayi tare da godiya da alkawarin bayar ta wasu muhimman gudummawa da zai ƙarfafa wannan waje.

Sai wakilin mai martaba sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Huhu Bamalli Hakimin Basawa Barden ƙerarriyan Zazzau Injiniya Abubakar Haruna Bamalli shima ya nuna jin daɗi da wannan ƙoƙarin.

Akwai wakilin shugan ƙaramar hukumar Sabon Garin Honorable Abubakar Jamil Albani wato Honorable Abdulkarim Kamilu shima yayi fatan alheri da nuna goyon baya akan wannan muhimmin aiki.

Sai sarkin Samaru Alhaji Dauda Abubakar da limamin babban masallacin garin Samaru Sheik Shanwel Zamansu sai hakimai da sarakuna da kungiyoyi da yan kasuwa da wakilan cibiyoyin kiwon lafiya daga jiha da ƙaramar hukuma duk sunyi farin ciki da kawo wannan asibitin mai tarihi.

Daga karshe Gidan jaridar Hausa Media Reporters da kungiyar ci gaban garin Samaru sun karrama Admiral Ibrahim A Dewu bisa kishin da ya nuna na kawo wannan asibitin garin samaru don amfanin al’umma.

Anyi taro lafiya an tashi Lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here