Aƙalla mutum 13 sun mutu sakamakon ruftawar wajen haƙar ma’adanai
Akalla mutane 13 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani wurin hakar ma’adinai a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Wani jami’in gwamnati a jihar, Joshua Riti, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu na Turkiyya a ranar Talata cewa waɗanda abin ya shafa ‘yan shekaru tsakanin 18 zuwa 30 ne kuma ‘yan ƙaramar hukumar Bassa ne.
Ya ƙara da cewa, rugujewar ta afku ne a ranar Asabar a kan iyakokin kananan hukumomin Bassa, Jos ta Kudu, da Jos ta Arewa, inda wadannan matasa suke neman abin dogaro da kai a cikin ramin haƙar ma’adinai.
KU KUMA KARANTA: Najeriya za ta ba da lasisin haƙar ma’adinai ga kamfanonin da ke aiki cikin ƙasar
A baya-bayan nan masu haƙar ma’adinai 22 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani ramin hakar ma’adinai a wani haramtaccen wuri da ke cikin wani wurin gandun namun daji da ke yankin karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba da kuma karamar hukumar Toungo a jihar Adamawa.