Aƙalla masu zanga-zanga 700 aka kama a Najeriya

0
74
Aƙalla masu zanga-zanga 700 aka kama a Najeriya
Link daftar PVP777
Link daftar Slot DANA
Link daftar PVP777
Link daftar Slot DANA

Aƙalla masu zanga-zanga 700 aka kama a Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama gomman masu zanga-zanga a ranar Asabar tare da harba barkonon tsohuwa don wargaza masu zanga- zangar da suka yi yunƙurin zuwa ofisoshin gwamnati da ke Abuja, babban birnin ƙasar, a rana ta uku ta zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake yi a kusan faɗin ƙasar.

A jihar Kano da ke arewacin ƙasar, an harbi aƙalla mutum ɗaya a wuya kuma an garzaya da shi asibiti, a cewar wani da ya shaida lamarin.

Mutane 13 ne dai aka kashe a ranar Alhamis a lokacin da zanga-zangar ta rikide ta koma tashin hankali, a cewar ƙungiyar rajin kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International, wacce ta zargi ‘yan sanda da yin amfani da harsasai kan masu zanga-zangar.

KU KUMA KARANTA: Jawabin Shugaba Tinubu kan zanga-zanga a Najeriya

A ranar Asabar ‘yan sanda sun faɗi cewa mutane bakwai suka mutu a zanga-zangar cikin kwanaki uku, amma basu ɗauki alhakin kisan ba.

An kama kusan mutane 700 a yayin zanga-zangar, bayan haka jami’an tsaro 9 sun jikkata, a cewar sanarwar ‘yan sandan.

A ranar Asabar masu zanga-zangar sun tattaru a wani babban filin wasa da ke Abuja amma ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen wargazasu a lokacin da suka yi yunkurin yin tattaki akan wata babbar hanya zuwa tsakiyar birnin.