Aƙalla mutum 20 sun mutu a Bayelsa bayan da kwale-kwalensu ya kama da wuta

0
73
Aƙalla mutum 20 sun mutu a Bayelsa bayan da kwale-kwalensu ya kama da wuta

Aƙalla mutum 20 sun mutu a Bayelsa bayan da kwale-kwalensu ya kama da wuta

Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kama wuta tare da fashewa da wani kwale-kwalen katako da suke ciki ya yi a jihar Bayelsa a ranar Laraba, in ji ‘yan sanda

Kwale-kwalen na ɗauke ne da ‘yan kasuwar da ke kai kaya yankunan da ke gaɓar teku, a cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Bayelsa, Musa Muhammed a ranar Alhamis.

‘Yan kasuwa kan je yankunan da ke gaɓar teku da kuma babban birnin jihar Yenagoa a duk mako.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 90 a Mozambik

Aƙalla mutum 200 ne rahotanni suka ce sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a Najeriya a bara kawai, inda hukumomi ke cewa ana yawan samun hakan ne saboda lodi mai yawa da rashin kula da jiragen ruwan.