Jirgin rundunar sojin sama ya yi hatsari a jihar Neja
Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin saman rundunar sojin sama ya yi hatsari a wani kauye da ke cikin ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin jirgin sama ya yi sanadiyar mutuwar mutum 18
Jaridar TheCable ta rawaito cewa matuƙa biyu sun tsira daga jirgin kafin ya faɗi kusa da ƙauyen Karabonde.









